Daga Mohamed Touzani
Al'ummar Moroko za su jima suna tunawa bala'in da suka shiga da yammacin ranar 7 ga watan Satumba 2023, yayin da ƙasa ta yi wata girgiza mai ƙarfi da misalin karfe 11:30 na dare (GMT+1) a wannan yanki mai yawan duwatsu, kusa da sanannen birnin yawon shakatawa na Marrakech, har ma da garuruwa da yawa a yankunan tsakiya da arewacin ƙasar.
Dubban a waje suka kwana saboda tsoron kar su faɗa irin halin da ƴan'uwansu suka faɗa, waɗanda ɓaraguzan gini suka binne su ko kuma suka rasa mahallansu bayan gidajensu masu ɗan dama-dama sun rushe.
Amma washe gari, wani irin shauƙin ƙarfafawa da bayar da goyon baya, da mutanen gari suka bai wa mutanen da masifar ta afka wa, ya kawar da tsoro da fargaba.
Halin tausaya wa waɗanda abin ya ritsa da su ya bazu zuwa duk manyan birane, da ƙauyuka da kuma garuruwan ƙasar, inda ake ta karɓar kayan abinci da magunguna da madara da tantuna da kuma suturu.
Ya wajaba a bayyana cewa, al'ummar Moroko sun taimaka tsakani da Allah, wajen kyautata wa waɗanda girgizar ƙasar ta shafa a wannan mawuyacin lokaci da kuma tallafa musu wajen kare su daga rauninsu.
Baya ga roƙon neman taimako da waɗanda bala'in ya shafa a farko-farkon faruwar iftila'in, da kuma watsawa da aka yi a kafofin sadarwa na zamani.
Ƴan Moroko mazauna ƙasashen waje masu matuƙar ƙarfin faɗa a ji, su ma sun yaɗa neman tallafin sosai, inda suka ƙaddamar da shirin tattara magunguna da kayayyaki da kuma tantuna a duk ƙasashen da suke zaune.
An nuna hotunan motocin dakon kaya maƙare da ton ton na abinci da barguna, suna ta kutsawa kan hanyoyin masu wahalar biyuwa a tasoshin talabijin a faɗin duniya.
Ƙin amincewa da mahukuntan Moroko suka yi na karɓar tallafi daga ƙasashen duniya - duk da sun zaƙu su nuna wa duniya za su iya gudanar da aikin ceto da kuɗinsu - ya tayar da ƙura a gun wasu ƙasashen kamar Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron bai ji daɗin amincewa da kayan agaji da Daular ta Moroko ta yi daga wajen Sipaniya, da Birtaniya, da Saudi Arabiya da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma ƙin amincewarta da abin da ƙasarsa, tsohuwar, uwargijiyar Moroko ta mulkin mallaka ta bayar.
Kafofin watsa labaran Faransa suna kallon ƙin amincewa da mahukuntan Moroko suka yi a matsayin nuna fushin Rabbat game da fuska biyu da Faransa take yi a kan batun Yammacin Sahara da kuma ɗasawa da take yi da Aljeriya, wacce ke goyon bayan samun ƴancin kan yankin.
Yayin da Daular ta ƙi amincewa da tayin agaji daga wasu ƙasashen, amma ba haka abin yake ba game da Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa masu zaman kansu da suka bayar da gudunmawar gogewar da suka samu a wasu ƙasashen da nahiyoyi wajen nemo masu sauran rai da kuma zaƙulo gawarwaki daga ɓaraguzai.
Wannan shi ne ya faru da Hukumar Agajin Gaggawa ta Turkiyya (IHH), wacce ta kutsa ƙauyuka dadama a yankin domin kawo wa mutane sassauci a yankunan masu yawan tsaunuka da girgizar ƙasar mai ƙarfin digiri 7 a ma'aunin Richter ta ɗaiɗaita.
Masu aikin sa-kai na hukumar sun raba abinci da barguna da kuma kayan tsafta ga mata da ƴaƴansu, waɗanda su abin ya fi shafa.
Ƙungiyoyin ba da Agaji na Turkiyya suna da ƙwarewa sosai a wannan fagen, lura da cewa su suka yi aiki a ayyukan jin-ƙai a Turkiyya da wasu ƙasashen da iftila'i ya faɗawa, musamman, ma a Derna, a arewa maso gabashin Libya, bayan wucewar mummunar guguwa Daniel.
Kwana ɗaya da faruwar bala'in, shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya bayyana alhininsa ga ƴan'uwa, al'ummar Moroko da kuma goyon bayan al'ummar Turkiyya a wannan mawuyacin lokacin.
"Allah ya ji ƙan waɗanda suka mutu, kuma ina yi wa waɗanda suka ji ciwo fatan warkewa cikin hanzari. Mana taimaka wa ƴan'uwanmu na Moroko ta duk wata hanya da za mu iya a wannan mawuyaciyar rana", shugaban ƙasar Turkiyya ya rubuta a shafin x (wanda a da aka sani daTwitter)
A ƙarshe, bayan ƴan matsalolin a ƴan ranakun farko da faruwar bala'in, an shirya aikin agajin kuma aka ƙara ƙaimi tare da taimakon tawagogi daga waɗannan ƙasashen da kuma ƙungiyoyin ba da agaji na ƙasa da ƙasa.
Hakan ya sa an gyara hanyoyin da suka yanke domin zirga-zirgar motoci, ɗaruruwan mutane a ceto su daga ƙarƙashin ɓaraguzai, a samar da matsugunai ga waɗanda suka rasa muhallansu, tare da samar da magani ga waɗanda suka jikkata a girgizar ƙasar.
A wani ɓangare na wannan ƙoƙarin, rundunar sojin ta Moroko ta kafa asibitocin tafi-da-gidanka masu ɗan dama da suke bayar da kulawa a kowane ɓangaren ƙwarewa, da ya haɗa da bayar da taimakon saita tunani ga waɗanda suka rasa makusantansu a daren wannan ranar firgicin na 7 ga watan Satumba.
Amma yayin da ake kammala aikin ceto, ya kamata cikin gaggawa a fara gagarumin aikin sake tsugunar da waɗanda abin ya shafa da kuma sake gina gidaje da yankunan da girgizar ƙasar ta ɗaiɗaita.
"Asusu na musamman domin magance mummunan tasirin girgizar ƙasar da ta afka wa Daular Moroko", an kafa shi ne da hadafin ya dinga karɓar gudunmawa daga mutanen ƙasa, da kamfanoni masu zaman kansu da kuma hukumomi.
Asusun ya tara sama da dirham biliyan 11 a matsayin gudummawa (kusan dala biliyan 1.2), baya ga kuɗaɗen da gwamnati ta tara domin gudanar da ayyukan gaggawa wajen gyare-gyare da sake gina gidajen da girgizar ƙasa ta Al Haouz ta lalata.
Gwamnati ta yanke shawarar ta bayar da tallafin kuɗin kai-tsaye na dirham 140,000 ($14,000) domin sake gina gidajen da suka rushe kwata kwata, da kuma dirham 80,000 ($8,000) domin ɗaukar ɗaainiyar gyaran gidajen da suka ɗan lalace.
Waɗanda suka rasa muhallansu, har ila yau, za su dinga karɓar alawus ɗin dirham 2,500 ($250) kowane wata, na tsawon shekara ɗaya, har izuwa lokacin da za a sake gina musu gidajensu.
An kafa wata "Hukumar Raya Yankin Atlas", yankin da girgizar ƙasar ta afka wa, domin ya tsara yadda za a tafiyar da aikin gyara da sake gina gidaje, yayin da zai yi la'akari da yanayin yankin da al'adun da aka gada da kuma ɗabi'un mutanen yankin," a cewar hukumomin Moroko.
"Hadafin shi ne a aiwatar da ayyukan bunƙasa zamantakewa da tattalin arziƙi a waɗannan yankuna," wannan majiyar dai ta ƙara da cewa.
Watanni uku da faruwar girgizar ƙasar,an soma aikin sake gina gidaje a duk yankunan da abin da shafa, tare da taimakon ƙwarewa daga hukumomi, waɗanda yanzu suke sa ido don ganin an yi biyayya ga ƙaidojin da aka gindaya na kiyaye motsin ƙasa.
Lokacin sanyi na ƙaratowa cikin hanzari kuma tsaunikan da ke yankin sun fara karɓar dusar ƙanƙarasu ta farko.