Daga Ma'aikaci
Dubban mutane a Nijar da Burkina Faso da Mali sun yi tattaki a ranar Talata domin murna bayan ƙasashen nasu sun fice daga Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka wato ECOWAS.
Ficewar tasu daga ƙungiyar ta fara ne a ranar 29 ga watan Janairun 2025, wato wata guda daidai bayan sun sanar da niyyar ficewarsu a daidai lokacin da ake cikin zaman ɗar-ɗar tsakaninsu da makwabtansu.
Ƙasashen uku na yankin Sahel waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soji sun haɗa wata sabuwar ƙungiya tasu mai suna Alliance of Sahel States wato AES, inda suke zargin ECOWAS da yi musu rashin adalci.
Rabuwar da aka yi zuwa yanzu ta yi tasiri matuƙa ta fannin tattalin arziki, inda ECOWAS ta rasa kaso 53 cikin 100 na girman ƙasarta da kuma rasa kusan 20 na jama'arta.
Amincewa da fasfo
A wata sanarwa, ECOWAS ta amince da ficewar ƙasashen uku. Sai dai ta buƙaci hukumomi da ke ciki da wajen ECOWAS su ci gaba da amincewa da fasfo ɗin 'yan ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar mai ɗauke da tambarin ECOWAS, da kuma barin 'yan ƙasashen shige da fice ba tare da biza ba.
Haka kuma ECOWAS ɗin na so a ci gaba da kasuwanci maras shinge a yankin Yammacin Afirkar kamar yadda tsarin na ƙungiyar ya tanada.
Sai dai kuma shugabannin ƙasashen Sahel - Janar Assimi Goita na Mali da Janar Abdourahamane Tiani na Nijar da Kyaftin Ibrahim Traore na Burkina Faso - na son tabbatar da ikonsu da bunkasa tattalin arzikinsu.
Kafa sabuwar rundunar soji
Ƙasashen sun sanar da kafa runduna mai dakaru 5,000 domin magance matsalar 'yan bindiga, da samar da sabon fasfo da kuma yanke hulɗa da ƙasar da ta musu mulkin mallaka wato Faransa.
Sai dai ƙasashen sun ci gaba da yunƙurin ƙara bunƙasa tattalin arziƙinsu da tsaro ta hanyar haɗaka da wasu ƙasashen da suka haɗa da Turkiyya da Rasha.
ECOWAS, wadda ke da hedkwata a Abuja babban birnin Nijeriya, an kafa ta ne a 1976 domin ƙara haɓaka tattalin arziƙin ƙasashen yankin. A tsawon shekarun da suka gabata, ta ƙara sauyawa, inda muradunta suka ƙara da haɗin kai ta ɓangaren siyasa da kuma soji.
Sai dai ƙasashen da suka ɓalle na zargin ƙungiyar ta ECOWAS ta zama 'yan amshin shatar Faransa da kuma saka musu takunkumi mai ƙarfi.
Ƙasashen uku sun ji haushi bayan ƙungiyar ta ECOWAS ta yi barazanar amfani da ƙarfin soji domin mayar da Nijar kan mulkin dimokuradiyya bayan an yi juyin mulki a ƙasar a 2023.
Tasirin ƙasashen yamma
Ƙungiyar ECOWAS ta sha musanta zargin da ake yi mata na cewa ƙasashen Yamma na juya ta.
Wannan ne karo na farko da mambobin ƙasashen ECOWAS da dama na ficewa daga ECOWAS. Ƙasar da ta bar ƙungiyar ta ƙarshe ita ce Mauritania a Disambar 2000.
A daidai lokacin da Burkina Faso da Nijar da Mali suka ɓalle, sauran ƙasashen na ECOWAS da suka yi saura sun haɗa da Benin da Cabo Verde da Cote d'Ivoire da The Gambia da Ghana da Guinea da Guinea-Bissau da Lberia da Nijeriya da Senegal da Saliyo da kuma Togo.
Sakamakon yadda ake samun sauye-sauye ta ɓangaren tattalin arziƙi da tsaro, babu tabbaci kan makomar ƙungiyoyin na ECOWAS da AES, amma kowace daga cikinsu na da yaƙinin tana kan hanya mai ɓullewa.