Yayin da Afirka ke samar da mafi yawan kokon da ake amfani da shi wajen hada cakuleti, ribar da yankin ke samu ita ce kusan kashi 3 cikin 100  na darajar kayan da ake fitarwa. Hoto: Reuters  

Daga Abdulwasiu Hassan

Masana'antar sarrafa cakuleti na cikin tsaka-mai-wuya sakamakon raguwar noman koko a kasashen yammacin Afirka abin da ya sanya farashin kokon ya yi tashin gwauron zabi da ba taba ganin irinsa ba.

Farashin tan ɗaya na koko - wanda aka cire daga nau'in waken cocao Theobroma - ya ninka fiye da sau biyu a watannin farko na shekarar 2024 sannan ya ninka sau uku a bara zuwa kusan dala 10,000.

Hauhawar farashin ta yi matukar shafar masu sarrafa cakuleti da masu saye, hakan ya bayyana ne a farashin fitattun samfura cakulati kamar Easter eggs da cakuleti bunnies wadanda suka karu da kashi 50 cikin 100 a kusan shekara daya.

A takaice, hakan na nufin tan ɗaya na koko a yanzu darajarsa ta ninka sau 11 fiye da farashin man fetur, inda ya zama babban hanyar samun kuɗaɗen waje ga ƙasashen yammacin Afirka kamar Nijeriya.

Shin, hakan na nufin wannan babbar matsalar da ba a taɓa ganin irinta ba a fannin samarwa da kuma kasuwancin koko, za ta iya samar da gagarumin ci-gaba ga nahiyar?

Kasar Ghana da Ivory Coast da Nijeriya da kuma Kamaru, suna samar da kusan kashi 75 cikin 100 na kokon da ake amfani da shi a duniya, a hikimance wadannan kasashen su za su fi cin moriyar hauhawar farashin albarkatun na koko.

A zahirance, noman koko ya fi wahala fiye da sana'ar hada cakuleti.

Kasar Ghana da Ivory Coast da Nijeriya, da kuma Kamaru suna samar da kusan kashi 75 cikin 100 na kokon duniya baki daya. / Hoto: Reuters

Raguwar koko

Tun da babban abin da ke haifar da hauhawar farashin koko shi ne raguwar nomansa, akwai yiyuwar a samu ragi a gwargwadon ribar da masu nomansa za su iya samu daga hauhawar farashin duniya kai-tsaye.

Mabambantan ra'ayoyi sun danganta raguwar samar da koko kan wasu abubuwa kamar hakar gwal ba bisa ka'ida ba, sauyin yanayi da tsufa, gonaki masu fama da cututtuka.

Hukumar sayar da koko ta Ghana, Cocobod, ta yi kiyasin cewa hekta 590,000 na gonaki sun kamu da cutar swollen ​shoot, wata kwayar cuta da ke kashe amfanin koko gaba daya, a cewar wani rahoto da Reuters ta fitar.

Wannan matsalar da wasu daban za su taka rawa a tsarin samar da koko a cikin watanni masu zuwa a duniya.

Kungiyar Cocoa ta Duniya ta kiyasta cewa, za a samu ragin kashi 11 cikin 100 na koko a kakar bana, lamarin da zai kara gibin wadatarsa.

Mabambantan ra'ayoyi

Yayin da matsalar karancin koko ke ta'azzara, ana sa ran samun sauki daga manoma da kawo yanzu gonakinsu suka tsallake rijiya da baya daga matsalolin da suka shafi sauran masana'antun.

Ko da yake har yanzu ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da karin farashin daga hukumomin koko na manyan kasashen da ke noman irin waken, amma tuni kasuwar Ivory Coast ta kara farashin albarkatun nomanta da kashi 50 cikin 100.

N'koh Ambroise, wani mai sarrafa cakuleti daga Ivory Coast, ya bayyana farin cikinsa game da hauhawar farashin koko a kasuwannin duniya. "Wannan abu ne mai kyau, wanda ya kamata ya zo tun da dadewa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Ambroise ba wai yana sarrafa nau'in cakuleti mai dadi ba ne kawai, fitaccen manomin koko ne a kasarsa. Nau'in waken kokon da yake samarwa daga gonarsa zai iya ninka farashin sauran irin kokon da aka fi samu sau biyar tun ma kafin farashin ya yi mummunar tashi.

"Idan dai batun farashin koko ne, zan iya cewa ya yi matukar tasiri a kasuwancina," in ji Ambroise.

Duk da cewa akwai mabambantan ra'ayoyi tsakanin masu sayen cakuleti da masu ruwa da tsaki a kasuwancin sarrafa koko, Ambroise ya bayyana cewa ba daidai ba ne nahiyar wadda ke samar da mafi yawan amfanin noman ta kasance abin da take samu bai wuce kashi 3 cikin 100 ba na ribar koko.

Mista Erneste Ogou, wani manomin koko, yana cire kwallon koko a wata gona a Alepe. Hoto: Reuters

"Da irin wannan farashin, a 'yan shekaru masu zuwa, ba za a samu gonar koko ko daya da za ta rage ba. 'Ya'yan masu sana'ar za su gwammace su yi wani abu daban fiye da ci gaba da abin da ba zai haifar musu da ɗa mai ido ba ko ya jawo musu asara," in ji shi.

Wasu sharhi na ganin hauhawar farashin abu ne mai kyau ga masana'antar, wadda kawo yanzu take samar da riba kadan ga manoma musamman a Afirka.

TRT Afrika