Daga Dayo Yussuf
Tsarin "bankin Musulunci", wanda kalmar tana nufin tsarin bankin wanda ake tafiyar da shi bisa tanadin shari'ar Musulunci, kuma yanzu yake tallata kansa ga kasashen Afirka a 'yan shekarun nan.
A Uganda, Babban bankin kasar a farkon wannan wata ya fitar da sanarwa cewa ya ba bankin Musulunci na farko a kasar lasisin fara aiki.
Nan take hakan ya jawo muhawara musamman a kafafen sada zumunta, tsakanin wadanda suke goyon bayan komawa kan tsarin bankin Musulunci wanda shari'a ta amince da shi da kuma wadanda ke son a ci gaba da amfani da tsarin bankin da aka saba da shi.
Saboda haka mene ne tsarin bankin Musulunci ko kuma bankuna da ke da tsarin hada-hadar kudi da shari'a ta amince da shi, mene ne abin da ya bambanta shi da tsarin da aka saba da shi?
Babban abin da aka fi ba muhimmanci shi ne gamsar da kwastomomi ta hanyar cajarsu kudi kalilan, wanda kuma ba ya mu'ammali da kudin ruwa.
Babu kudin gudanar da aikace-aikace
Tsawon shekara shida, Mohammed ya yi amfani da tsare-tsaren bankin Musulunci iri daban-daban inda yake da asusun ajiya, sai kawai ya sha mamaki lokacin da aka caje shi wasu kudi kan kudin da ya ranta.
"Sun ce ba su da tsarin karbar 'kudin ruwa' – cewa idan ka karbi rance, to ba za a caje ka kudin ruwa ba," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
"Amma idan ka kula sosai, za ka ga akwai wasu caje-caje kan aikin da aka yi maka, wanda suke kira riba."
Mohammed yana cikin kwastomomi da suke neman hanyar kaucewa tarin caje-caje kudin da bankuna suke yi wa kwastoma.
Mutane da dama a fadin duniya sun yanke kauna a kan bankuna, wadanda ake kallo a matsayin wadanda aka gina kan samun riba kacokan a kowane irin hali.
Masana sun yi gargadin cewa hatta bankunan da aka gina su bisa tsarin shari'ar Musulunci ba za su kasance kamar cibiyoyin bayar da agaji ba.
Madadin su kasance masu arha, babban ginshikin kafa su shi ne samar da "tsarin halal", wanda shari'ar Musulunci ta amince da shi.
"Mutane suna zuwa bankunan ne da tunanin cewa ba za a caje su kudin ruwa, ko kowane caji ba, wanda a ganinsu ba halal ba ne a shari'ar Musulunci," in ji Mohammed Issa wani masanin tattalin arziki a Tanzaniya.
"Kwastomomi suna son sauki ko kuma kada a caje su ko sisi kuma sun yi amannar cewa babu cajin kudi a tsarin. Ya kamata a gyara wannan tunanin. Ayyukan da banki suke yi wa kwastomomi ba kyauta ba ne."
Tsarin bankin Musulunci ya haramta cajin kudi ko karbar kudin ruwa kamar yadda ake yi a tsarin bankin da aka saba da shi.
Wani tanadi kuma shi ne fayyace komai yayin kulla yarjejeniya tsakanin bankin da kwastoma.
Tsarin ya haramta duk wata huldar kudi da ba ta dace da shari'ar ko koyarwa addinin Musulunci ba, ciki har da tsarin Investment Domain.
Karbuwarsa a fadin duniya
Manyan cibiyoyin kudin duniya kamar Bankin Duniya da Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya (IMF) da Asusun Ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai duk sun amince da shi.
Kasashe da yawa sun amince da tsarin bankin, wanda ba kawai don amfanin Musulmi aka yi shi ba. Sabanin yadda yawancin mutane suke tunani, tsarin bankin Musulunci kofofinsa a bude suke ga duk wanda yake son shiga a dama da shi.
"Idan ka lura za ka ga kasashe kamar Birtaniya sun yi nisa sosai wajen samar da tsarin bankin Musulunci fiye da kowace kasa bayan Kasashen Larabawa," kamar yadda Issa ya shaida wa TRT Afrika.
"A shekarar 2009, marigayi Fafaroma Benedict XVI ya shawarci bankuna da su rika amfani da tsarin bankin Musulunci saboda samun karin aminci daga kwastomominsu, wanda suka rasa hakan saboda kudin ruwan da suke caja masu yawa a kan bashi," kamar yadda masanin ya bayyana.
Har ila yau Issa ya ce kasar Malesiya, wacce har zuwa bara kaso 30 cikin 100 na kwastomomin bankin tsarin Musulunci a kasar ba Musulmi ba ne. Haka abin yake a Afirka ta Kudu da Tanzaniya da Kenya da kuma Uganda.
"Tsarin bankin Musulunci ya samar da tabbaci. Idan ka kulla yarjejeniya da bankin cewa riba za ta kasance wani kaso ne, kuma ba za ta taba canjawa ba – ko da bayan shekara biyar ko 10 ko kuma 20," kamar yadda Issa ya yi bayani.
Tsarin tafiyar da bankin
Abin da ke bayar da mamaki dangane da tsarin bankin Musulunci shi ne yadda ake tafiyar da bankin ba tare da rushewa ba.
Riba, sabanin kudin ruwa, ana samun ta ne da cajin kudin da ake wa kwastomomi bayan aikin da bankin ya yi musu, wanda hakan ya dogara ne kan sauye-sauye da ke faruwa a kasar a lokacin, kamar darajar kudi da sauran abubuwa.
A wasu wurare, bankuna suna zuba jari na hadin gwiwa tare da kwastomomi kuma sai su raba ribar ko asarar komai ya danganta ne a kan kason da aka yi yarjejeniya a kai.
Issa ya ce kusan duka bankunan da ke kasashen da ke arewa da Sahara suna da tsarin bankin Musulunci. "Nijeriya da Senegal da Mali da Gambiya da Nijar su ma suna da tsarin.
A yankin kudu da Sahara, Sudan ce kasa ta farko da ta samu bankin Musulunci." A yankin Gabashin Afirka kansa ya rungumi tsarin, inda Kenya ta fara a shekarar 2005, daga nan sai Tanzaniya da Burundi da Rwanda yanzu kuma Uganda.
Zambiya da Zimbabwe sun yi kokarin kwatanta fara tsarin a baya-bayan nan, kuma karin kasashe za su biyo sahu.
Kaddamar da tsarin takardun Bonds na Musulunci, wanda yake bukatar farawa da wani tsarin hada-hadar kudi, hakan ya sa tsarin ya kara samun karbuwa.
Ko da yake tsarin bankin Musulunci yana ci gaba da yaduwa cikin sauri, sai dai har yanzu akwai sauran aiki a gaba.
Masana sun ce babban kalubalen shi ne aiwatar da tsarin a kasashen da ba na Musulmi ba, galibi saboda tsare-tsaren da ke cin karo da juna kan yadda za a yi aiki da tsarin hada-hadar kudi.
"Akwai bukatar a samu gagarumin sauyi a bangaren tsare-tsaren kudi da kuma sauyi ka'idojin kashe kudi da dokokin haraji saboda a iya amfani da wadannan tsare-tsaren," in ji Issa.
Bisa la'akari da wadannan tanade-tanade, matakin da Uganda ta dauka kan gyara dokar hada-hadar kudi ya taimaka wajen rage kalubalen da ke jawo cikas kan aiwatar da tsarin bankin Musulunci.