Daga Abdulwasiu Hassan
Masana'antar samarwa da sarrafa koko ta zama wane bangare mai girma a fannin noma a Afirka tun karni na 19, musamman a Yammacin Afirka da Kamaru.
A zamanin mulkin-mallaka, wadannan yankuna sun fara samar da koko, wanda ake fitar da shi kafin a sarrafa da inganta shi a wasu sassan duniya.
Shekaru 60 bayan kawo karshen mulkin mallaka, yanayin samar da koko a yankin bai wani sauya ba. Yammacin Afirka sun ci gaba da zama cibiyar samar da koko, suke samar da koko mafi yawa da ake bukata a duniya.
Jaridar Kungiyar Cocoa Ta Kasa da Kasa bugu na 4 game da kakar koko ta 2022-2023 ta ce kasashen Afirka; Cote d'Ivoire, Ghana, Njeriya da Kamaru kadai na samar da kaso 73 na kokon da ake bukata a duniya.
Duk da kasancewar Afirka cibiyar samar da cocoa, yankin na cin gajiyar wani adadin dan kankani ne na arzikin koko din, kamar yadda kwararru suka bayyana.
Kamar yadda manajan Bankin FIta da Shigar Da Kayayyaki na Nijeriya Abba Bello ya bayyana a wajen Taron Kasa da Kasa kan Cocoa da Chakulet da aka gudanar a Abuja da Lagos a kwanakin baya, masana'antar cocoa - da suka hada da cake da chakulet - sun kai darajar dala biliyan $200.
Alkaluman Cibiyar Kasuwanci ta Duniya sun nuna irin bambanci amfana da cocoa da ake samu kamar haka; "Abun takaici, dukkan cocoa da Yammacin Afirka ke samarwa a kasashen Cote d'Ivoire, Ghana, Nigeria da Kamaru na samun dala biliyan 10 kawai, yayin da sue fitar da kaso 70 zuwa 75 na cocoa din a duniya baki daya."
Nijeriya da ta samar da cocoa tan 208 a 2021, ta samu dala miliyan $628 ne kawai. Amma kuma a gefe guda, Jamus wadda ba ta samar da cocoa, ta samu dala biliyan 57.3 daga fitar da kayan da aka samar da cocoa zuwa kasashen waje.
Manyan matakan neman gyara
An dauki matakai da yin yunkuri da dama don taimakawa manoman Afirka da kasashe masu samar da cocoa don ganin sun samu damar fitar da waken da yawa.
Misali, an kafa hukumomin kula da sarrafa cocoa a kasashe irin su Ghana da Nijeriya don kara yawan ribar da manomanta ke samu.
A Nijeriya, an dauki babban mataki na habaka amfana da noman cocoa shekaru da dama da suka gabata, inda Gwamnatin Yankin Yamma ta gida Gidan Cocoa a Ibadan.
A 1965 aka kafa wannan hukuma wadda ita ce gini mafi tsayi a Yammacin Afirka, kuma har zuwa 1979 ginin ya zama mafi tsayi a Nijeriya.
Kasashen da ke da karsashin habaka ribar da suke samu wajen samar da cocoa, an kasar da Majalisar Cocoa ta Cote d'Ivoire-Ghana, shugabannin kasashen sun dora alhaki kan wannan Majalisa don kara yawan kudin waken cocoa.
Majalisar na da kuma manufar ganin manoma sun samu kudade da yawa daga noman da suke yi.
Mafita
A takaice dai, wannan kalubale na nan a Afirka inda ya rage ga nahiyar ta zage damtse wajen samun manyan kudade daga cocoa din da suke fitarwa. To, me yake sanya hakan ke da wahalar tunkara?
Dr Patrick Opoku Asuming, masanin tattalin arziki kuma babban malamin jami'a a Jami'ar Kasuwanci ta Ghana, na da ra'ayin cewa babbar hanyar kalubalantar wannan matsala ita ce duba ga wajen da ya dace.
"Akwai wasu 'yan abubuwa. Ina tunanin a yanzu ba mu mayar da hankali kan asalin inda ribar sayar da cocoa take ba," in ji Dr Asuming.
Ya kara da cewa har yanzu ana fitar da mafi yawan cocoa zuwa kasashen waje.
Kasashen da suke sarrafa cocoa su samar da abubuwa kamar chakulet su ne suka fi amfana sama da kowa.
"A baya-bayan nan, mun ga yadda Ghana da Cote d'Ivoire ta yi kokarin kafa wata hukuma da ba ta iya aikata wani katabus ba.
Ina tunanin idan muka ci gaba da mayar da hankali kan fitar da danyen cocoa zuwa kasashen waje, ba za mu samu wani amfani da yawa ba," in ji shi a yayin tattaunawa da TRT Afirka.
Dr Asuming ya kuma bayar da shawara da cewa kasashen Afirka za su iya amfana da yawaita bincike kan yadda za a iya amfani da bawo da rassan bishiyun koko wajen samar da wasu kayayyaki kamar sabulu.
Ya gamsu da cea hanzarta aiwatar da Yarjejeniyar kasuwanci ba Tare da Tsangwama ba a tsakanin kasashen Afirka za ta taimaka, inda za ta janyo a kai ga sarrafawa da amfani da koko a nahiyar.
Mafi yawan kwararru na bayar da shawarar cewa idan har ana son nahiyar ta habaka wajen samar da cakulet da kuma samun riba da yawa daga noman koko, tana bukatar tabbatar da samun ingantacciyar lantarki, sannan ta samar da madarar shanunta da kanta.
Da zarar an samu nasarar cim ma wadannan abubuwa, kwararru sun ce Afirka za ta fara mamaye harkokin samar da kayayyaki daga koko, wanda a yanzu kasashen da ba sa noma koko din ne suke cin gajiyar ta.