Daga Dayo Yusuf
Watan tara na Hijira a kalandar Musulunci wanda asalinsa ke nuna tarihin yadda Annabi Muhammad (S.W.A) ya yi ƙaura daga Makka zuwa Madina, a lokacin ne al'ummar Musulmai sama da biliyan 2.5 a fadin duniya suke azumi a watan Ramadan.
Ana gudanar da azumin ne har tsawon ranakun watan baki daya tun daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana tare da addu’o’i da kuma tunatarwa Kamar yadda koyarwar Annabi (S.A.A.W) ya bayyana.
Watan Ramadan ba wai kawai yana kara wa muminai ayyukan ibada da kuma tunarwa ba ne, falalal cikin wata mai alfarma yana ciyar da gangan jiki da tunani gwargwadon yadda yake tsarkake ruhi.
Lokaci ne na musamman na kamewa da kuma yin ibada da mubaya'a da ya hada biki na ibada da kuma iyali, da al'umma a lokaci guda.
Azumin Watan Ramadan
A cewar Alƙur'ani mai tsarki, azumi wani nau'i ne na ibada da aka wajabtawa dukkan muminai.
“Ya ku waɗanda kuka yi imani, an wajabta azumi a kanku, kamar yadda aka wajabta wa waɗanda suka gabace ku, saboda ku zama tsarkarku,” a cewar wata aya daga Suratul al-Baqarah a cikin Alƙur’ani.
A cewar malaman addinin Musulunci, azumi wajibi ne a watan Ramadan kuma yana da fa'idodi da falala masu yawa ga kowane mutum.
''Wannan ne watan da mutane za su nemi gafarar Allah a kan kurakuran da suka aikata, sannan suna amfani da wannan damar wajen kyautatawa iyalansu da abokansu da kuma al'ummar da suke rayuwa a cikinta," kamar yadda malamin addinin Islama da ke Nairobi Sheikh Shaaban Ismail ya shaida wa TRT Hausa
"Duk musulmin da ya kai shekarun balaga ko sama da haka, ban da wasu ƴan tsiraru, wajibi ne su yi azumi."
Shika-shikan Musulunci
Azumin watan Ramadan na daya daga shika-shikan Musulunci guda biyar, wadanda wajibi ne ga dukkan Musulmai su yi riko da su.
Na farko shi ne "shahada", ko kuma kalmar imani da cewa Allah shi ne abin bautawa shi kadai, kuma Annabi Muhammadu manzonsa ne.
Na biyu shi ne tsayar da salloli biyar a rana sai kuma Azumi a watan Ramadan da bayar da "zakka" (aikin ba da sadaka), da kuma ziyarar Makka don yin aikin Hajjin ga wadanda suke da halin zuwa.
Iyaye Musulmai gaba ɗaya sukan koyar da ƴaƴansu tun suna ƙanana ɗaukar azumin watan Ramadan a matsayin umarni daga Ubangiji, da nufin amfanar da su ta hanyar wadatar da kowane fanni na rayuwarsu.
“Wasu daga cikin wadanda azumin bai wajaba a kansu ba sune tsoffi da marasa karfi da suka hada da masu fama da lalurar ajali, a maimakon haka ana bukatar su ciyar da miskini abinci duk ranar wata,” in ji Sheikh Shaaban.
“Idan mutum yana fama da wata rashin lafiya na ɗan wani lokaci ko kuma ya kasance matafiyi ko kuma mai ciki ko mai shayarwa, ko mai jinin haila, an kebe masu irin wannan lalura daga yin azumi, tare da gargadi kan cewa sai mutum ya rama ta hanyar sake yin azumin daga baya”.
Faɗaɗa ayyuka
Azumin Ramadan ba wai kawai kaurace wa ci da sha ba ne. Dole muminai su kaurace wa sha'awarsu kamar yin jima'i. Ana kuma bukatar musulmi su kara taimakawa marasa karfi a cikin watan.
A bayyane yake cewa a tsawon shekaru har wasu da ba musulmai ba sun yarda tare da shaida muhimmancin watan Ramadan.
A fadin duniya baki daya, wasu wadanda ba musulmi ba su kan yi azumi a cikin watan Ramadana mai tsarki- wasu don samun biyan bukatu na ruhinsu da kuma kebe kawunansu don tarbiyyar da ke tattare da watan, wasu kuma don su ji yanayin da ake ji, wasu kuma a matsayin sadaukarwa ga mutanen da ke kusa da su.
"Ana so Musulmai su nisanci duk wani aiki na zunubi ko kuma na rashin ɗa'a a kowane lokaci, sannan a cikin wannan wata ana bukatar su fadada ayyukansu na alkhairi da kuma gujewa duk wata shagala ko wacce iri ce.
"Idan aka kiyaye, hakan zai kawo zaman lafiya da wadata a cikin al'umma gaba daya," a cewar Sheikh Shaaban.
Al'adar buda Iftar, ko buda baki bayan faduwar rana a kowace rana, wani bangare ne na watan Ramadan wanda ya zarce iya addini kawai.
A mafi yawan lokuta, mutane kan gayyaci ’yan uwa da makwabta da abokan arziki domin su buda baki tare ta hanyar cin nau'in abinci irin daban-daban gami har ma wasu na musamman da ake ci a lokacin Ramadan.
Don haka, lokacin buda baki ba wai dabi'a ce ta buda baki kawai ba, hanya ce ta hada kai da kuma kara ɗankon soyayya da kautatawa a tsakanin al'umma.