Masana sun yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar ƴan zamanin gaba ba za su samu damar ganin zakuna ba sai dai a hoton cikin littafe, masana sun yi gargaɗi. / Hoto: AP / Hotuna: Getty Images      

Daga Sylvia Chebet

Kowane yaƙi yana da gwarzonsa, Labarin dawowar zakuna a manyan dazukan Afirka ba zai taɓa dadi ba, ba tare da la'akari da gagarumin gudumawar da kungiyar 'Lioness' ta bayar ba.

Eunice Peneti, mai shekara 30, ita ce mace ta farko da ke shugabantar wani rukunin dazukan Kenya na Amboseli, yankin da ke dauke da ɗimbin namun daji iri daban-daban, kana yana kewaye da Dutsen Kilimanjaro daga nesa.

Peneti da tawagarta sun ci gaba da gyara ciyayin dajin mai faɗi, suna kokarin kare sarkin daji daga haɗuran farauta ko na wani guba.

Tasirin ayyukan kungiyar 'Lioness' ya biyo bayan haɓakar zakunan Kenya da aka samu bayan raguwarsu a tsawon shekaru goma - an samu karin kashi 25 cikin 1000 tsakanin shekarar 2010 zuwa 2021.

Alkaluman da hukumar kula da namun daji ta Kenya ta fitar sun nuna cewa adadin zakuna na kasar da ke yankin gabashin Afirka a shekarar 2021 ya kai 2,589.

Sakamakon irin wannan ƙoƙari na kariya da kiyayewa yana da na shi kalubalen, duk da cewa ko wannensu bai zo cikin sauki ba.

Peneti na sane da wannan kalubale fiye da kowa, duk da zurfin iliminta na sanin halayyar zaki da kuma haɗuran da ke tattare da manyan dabbobi nau'in maguna, ta kan yi sintiri cikin dajin tare da hadin gwiwar tawagarta ta mata a kowace rana.

A takaice sintirin tawagar yana da sauƙi: idan har suka kasance tare ba tare da barin juna ba ko na ɗan lokaci.

"Kasancewarmu a cikin dajin yana hana masu kokarin cutar da dabbobin aika-aikansu. Ta hanyar sintiri da kuma hulda da jama'ar yankin, muna tabbacin cewa wadannan zakuna za su iya rayuwa da bunkasuwa cikin yanayi mai aminci," kamar yadda Peneti ta shaida wa TRT Afrika.

Ruri ko kukan zaki a cikin daji

Kimanin zakuna 25,000 ne ke yawo a cikin daji a yanzu, adadin da ya ragu daga 200,000 a shekaru  goma da suka wuce. / Hoto: hukumar Kariyar Dabbobi ta Duniya

Ga Peneti da tawagarta, babu wani abu da ya fi gamsar da su fiye da ganin zakuna zaune cikin zaman lafiya da junansu a fadin daji.

Ta kan mai da hanlakinta ne kan zakunan da ke kwance a inuwar tare da 'ya'yansu, yayin da suke mai da hankali kan ganimar da suka yi farauta, ganin hakan ya kan kara mata nutsuwa.

"Akwai zakuna da dama, manya ko kanana. Hakan na nuna cewa adadin zakin yana karuwa," in ji ta.

Duk da cewa ana samun sakamako mai kyau a wurin adana namun daji na Kenya, lamarin ba haka yake ba a duniya.

An sanya zakuna cikin jajayen jerin nau'in dabbobi masu barazana.

Wani bincike da kungiyar kare namun daji ta duniya ya nuna cewa an samu raguwar kashi 43 cikin 100 na zakuna a Afirka tsakanin shekarar 1993 da 2014.

Asusun kula da namun daji na duniya (WWF) ya kiyasta cewa a yanzu haka zakuna 20,000 zuwa 25,000 ne kawai suka rage a cikin daji, kasa da kusan 200,000 a shakaru goma da ya wuce.

"A yanzu haka kasashe kalilan ne kawai muke iya samun zakuna." kamar yadda Edith Kabesiime, shugabar Hukumar Kare Dabbobi ta Duniya WWF ta shaidawa TRT A firka (WAP) inda ta kara da cewa " sai da kai ga kasar Rwanda ta yi jigilar zakuna tare da dawo da dazukan kasar."

David Mascall, kwararre a fannin kiwon zaki, ya yi gargadin cewa idan ba a yi komai akan hakan ba, makomar nau'in halittun a fadin Afirka zai yi rauni. "Al'ummar da ke gaba ba za ta samu damar ganin zaki ba sai dai a hoton cikin littafi."

Sandan Sihiri na farauta a Kenya

Yussuf Wato, manajan fannin bincike da sabbin shirye-shiryen nazarin halittu, a hukumar WWF-Kenya, ya danganta haɓakar da aka samu na zakunan Kenya da dabarun kiwo da kariya masu yawa da aka tanadar.

"Kungiyoyin samar da kariya sun aiwatar da tsare-tsare iri daban-daban don hana haɗuran namun daji ga ɗan adam kamar ''Predator-proof bomas'' katangar da aka kewaye wurare masu hadari da kuma sanduna farauta da fitulun zaki da al'ummar yankin suke amfani da su wajen kare mutane daga harin manyan dabbobin," in ji shi.

Predator-proof bomas, ƙaƙƙarfan shingaye ne da ke kare halittu daga zakuna da daddare, yayin da hasken fitulun zaki ke hana manyan dabbobin kusantar matsugunan da mutane suke.

Wani bincike da mujallar Frontiers in Conservation Science ta wallafa, an kariya gano cewa gatangar da aka kewaye wurare masu hadari su kan rage hare-hare kan dabbobin da ake kiwonsu da kashi 80 cikin 100.

Yayin da wani bincike kuma da mujallar Oryx ya wallafa ya nuna cewa fitulun zaki sukan rage hare-hare kan dabbobi da kashi 70 cikin 100.

Kazalika an samu karin yawan al'ummomin da ke kula da namun daji musamman a wajejen ba da kariya a yankunan da ke karkashin al'ummomin.

Ɗaya daga cikin misalan shirin samar da kariya ga al'umma da ya yi nasara shi ne na Ƙungiyar Kula da namun daji ta Maasai Mara, wacce ke da mutune 150 karkashinta.

Mazaunan Masai Mara na Kenya suna kewaye ne wurin adana namun daji na Masai Mara National Reserve zuwa yankin arewa da arewa maso gabas da kuma yankin gabas. Hoto: Reuters

Kabesiime ya bayyana tsarin samar da kariya da al'ummar Kenya ke jagoranta a matsayin wani "Sandan sihiri".

Mafita/matakai

Masana sun sha gargadin kasashe cewa kare sarkin daji (zaki ) ba abu ne da zai dace ba.

"Zakuna mafarauta ne, kuma suna zaune a kololuwar sarkar wuraren samun abinci. Hakan na nufin sun mamaye wani muhimmin bangare na dukkan halittun da ke fadin kasa, ta yadda duk wani abu da ya dagula yanayin muhallin zai dagula zakuna." a cewar Kabisiime.

Ta ba da misali da kasar Uganda, inda rikicin siyasa a shekarun1970 zuwa 1980 ya haifar da raguwar yawan namun daji saboda tabarbarewar doka da oda.

Wani abun mamaki da ya faru a lokacin shi ne, kusan zakuna 400 ne kacal suka rage a duk fadin Uganda.

Cibiyar kula da namun daji ta Uganda na shirin kafa wuraren kiwon zaki a wasu wuraren adana namun dajinta, sai dai hukumar WAP ta yi gargadi kan a yi taka-tsan-tsan kan wannan mataki, inda ta ce Afirka ta Kudu ba ta yi nasara kan hakan ba.

"Kiwon cikin keji da kuma ciyar da zakuna kai tsaye hanya ce da ba ta dace ba, mussaman wajen kokarin gyara wata matsala mai sarkakiya." in ji Kabisiime.

Ta ja hankali kan cewa, ta yaya za a koya wa zakuna hanyoyin zama manya mafarauta a wuraren da aka killace su?

Wani abu da ya fi ba ta mamaki shi ne yadda za a horar da ’ya’yan zakuna hawa kan bishiyoyin da ke Ishasha, wani fitaccen wuri da ke daukar hankali na Sarauniya Elizabeth da ke Uganda.

Kazalika idana aka saba ciyar da zakunan kai tsaye. hakan zai matukar tasiri wajen sauƙaƙa harinsu kan dabbobi da sauran halittu, yanayin da ka iya dagula rikicin ɗan adam da namun daji.

TRT Afrika