Masu kantinan da ake kira Spaza sun bayar da rahotannin shan wahala wajen yin rajistar shagunan nasu. Hoto: Jo'burg Metro Police Department

Daga Charles Mgbolu

An samu muhawara da cece-ku-ce bayan sanarwar da gwamnatin Afirka ta Kudu ta fita na kara wa'adin rajistar shagunan spaza da ke sayar da kayan ciye-ciye a fadin kasar sakamakon mutuwar yara kanana a yankuna da dama bayan sun ci kayan da ake sayarwa a shagunan.

A ranar Laraba, Ministan Kula da Kungiyoyi da Harkokin Al'adu Velenkosini Hlabisa ya sanar da an kara wa'adin rajistar zuwa 28 ga watan Fabrairun 2025, daga 17 ga Disamba da aka sanar za a rufe.

An samu tsaiko wajen rajistar a yankunan kasar da dama, inda masu shagunan spaza suka bayyana wahalar da suke sha wajen yin rajistar, inda suka bayyana matsalolin da ake samu a ofisoshin kananan hukumominsu, in ji tashar talabijin ta kasar.

Mamban majalisar Zartarwa, Lebogang Maile ya fada wa manema labarai ranar Alhamis cewa lardin Gauteng ya yi rajista ga shaguna sama da 25,000, amma an dawo da fom din shaguna 10,000.

'Ba zai yiwu ba'

Kungiyar 'Yan Kasuwa Bakar Fara ta Afirka ta Kudu (BBC) a ranar Alhamis sun yi maraba da kara wa'adin ga shagunan spaza, suna mai cewa ba za a iya cim ma me ake so ba a wa'adin baya da aka bayar.

Shugaban kungiyar Kganki Matabane ya sanar da tashar talabijin din kasar cewa "Mun riga mun san 17 ga Disamba da aka sanya a matsayin wa'adin rajistar ba mai yiwuwa ba ne, amma kamar yadda kuka sani, dole ne a matsa lamba kan tsarin.

Muna maraba da karin wa'adin ..... mun yarda da gwamnati cewa dole ne a matse loakcin don a tabbatar da kowa ya ji matsin."

Amma kara wa'adin ya janyo damuwa da cece-ku-ce musamman ga mazauna yankunan da aka fi samun mutuwar yara kanana bayan cin abincin da suka saya a shagunan spaza.

Ana zargin shagunan spaza mafi yawan su mallakin 'yan kasashen waje da sayar da kayan abincin da lokacin amfani da su ya kare wanda hakan ya janyo cututtukan lalata jini da asarar rayuka.

Hare-Hare kan shaguna

A watan Nuwamba, an kai hari kan shagunan spaza mallakin 'yan kasashen waje a gundumar Mangaung bayan wasu daliban firamare 47 sun kwanta a asibiti sakamakon cin biskit da ke da illa.

Shugaban Kungiyar Masu Shaguna da Gidajen Haya, Veli Khumalo ya fada wa SABC a ranar Laraba cewa za su ci gaba da aiki don tabbatar da 'yan gudun hijira da ba su da takardu ba su bude shagunan spaza ba a yayin da ake jiran wa'adin ya kawo karshe.

"Duk wadannan da ba a yi wa rajista ba ba za su bude hsagunan spaza ba. Za mu tabbatar da sun bar kasar nan, ba su cancanta ba.

Amma wadanda suke da takardu ko suka samu mafaka, za mu taimaka musu su y rajistar shagunansu."

Kara wa'adin rajistar ya janyo korafi da dama a shafukan sada zumunta.

"Bai kamata a samu dan gudun hijira ko mai neman mafaka ya bude kantin spaza ba. Mafi yawan 'yan gudun hijirar da ke cewa sun samu mafaka ba haka ba ne, suna zaune ba bisa ka'ida ba," wani ya rubuta a shafin X.

Tallafawa kasuwanci

Mahukuntan Afirka ta Kudu a wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba cewa sun fahimci damuwar 'yan kasar amma dole ta sanya su kara wa'adin saboda akwai bukatar taimaka wa masu kanana sana'o'i.

"Game da duba yiwuwar ko za a kara wa'adin rajistar, gwamnati ta yi duba ga kokarinta da take yi na taimaka wa masu kananan sana'o'i, ana bayar da fifiko ga tsafta da lafiyar jama'a, tabbatar da shigar da kowa da adalci da kuma ci gaba da kare martaba," in ji sanarwar.

Amma shin yin rajista ga shagunan spaza zai kawo karshen matsalar gurbatattun kayan abincin da ake sayarwa? wasu masu sharhi ba sa tunanin haka.

"Dole ne sashen kula da lafiya ya sanya idanu kan shagunan lokaci zuwa lokaci, kuma idan ba sa sayar da abin da ya dace, sai a rufe shagunan gaba daya ba tare da bata lokaci ba" in ji wani mai sharhi a rubutun da ya yi a shafin X.

Amma mahukuntan Afirka ta Kudu sun ce tabbas hakan za a dinga yi.

"Wadanda suka yi rajistar shagunansu tare da samun amincewa, dole ne su kuma sakr neman izinin gudanar da kasuwanci.

"Domin samun wannan lasisi, ma'aikatan lafiyar muhalli za su dinga sanya idanu kan shagunan da ke sayar da kayayyakin da ake ci," in ji sanarwar.

TRT Afrika