A Rwanda, ana sayar da kilo daya na kazar gidan gona kan dalar Amurka biyar. Hoto: Mbandinga

Daga Firmain Eric Mbadinga

Ko dai mutum ya zama wanda ba ya cin naman kaza sai ganyaye ko kuma idan ya ci naman na masa illa, to me zai hana a yi tunkaho da cin naman kaza?

Nikakkiya, basasshiya ko dafaffiya, kaza ta kasance sinadarin gina jiki mai sauki daga cikin kayan abinci, kuma wanda aka fi ci a kowacce rana tare da abinci a duniya baki daya.

Wasu nazarce-nazarce sun nuna nan da 2027, kaza z ata haura duk wani abinci a duniya da zai zama zabin jama'a, inda tan miliyan 117 zai dinga biyan bukatar da ake da ita.

A Rwanda ma, mutane na son naman kaza sosai.

A kasar da ke da yawan mutane miliyan 14, wadda ta illatu daga tasirin sauyin yanayi da ake samun ambaliyar ruwa da fari, tabbatar da kayan kiwo da suka hada da kaza, na fuskantar kalubale har ma ga wadanda ke aiki a bangaren.

A tsakanin watan Yuni da Oktoban 2024, mamakon ruwan saman da ba a saba gani ba a kasar ya janyo ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa, inda aka rasa rayuka da dama da dukiyoyi da ma amfanin gona.

Da yawa daga manoman karkara sun fuskanci matsalar mutuwar dabbobin da suke kiwo saboda mamakon ruwan sama.

Kafin ambaliyar ruwan, wannan masana'anta na fuskantar kalubalen gibin kasuwanci, wanda ke bayyana wa karara yadda suka yi tsada ga masu saye.

A Rwanda, farashin kilo guda na kazar gidan gona a shaguna ya tashi zuwa dalar Amurka biyar, wanda ya sanya jama'a da dama ba za su iya saya ba.

Babu mamaki cewa a kasar da ke da Dubunnan Tsaunuka, yawan abincin dabobin da ake kiwata wa da kowanne dan kasa ke ci a shekara ya haura kilo guda.

Bayan afkuwar ambaliyar ruwa a lokuta daban-daban, masu gidajen gona da ke karkara sun tafka asara saboda mutuwar kajinsu. Hoto: Mbandinga

Shiga harkokin kiwo

To ta yaya gidaje da suke bukatar sinadarin protein a abincinsu suke fama a lokacin da tashin farashin ke hana su sayen naman kaza?

Michel Christophe Mbadinga, wani jami'in diplomasiyya a Gabon na son rugumar kasuwancin cikin rashin tabbas domin nema hanyoyin warware matsalar.

A 2022, Michel Christophe ya kafa gidan gonar kaji a wajen birnin Kigali, babban birnin kasar.

Ya kira wannan kasuwanci nasa da sunan Kazar Kauye, wanda tsohon ma'aikacin gwamnatin ya cika burinsa na rayuwa.

Tun da fari dai, ayyukan gidan gonar sun hada da kiwa ta kaji don su yi kwai. Bayan shekara guda, Michel ya fara kiwon kajin da kawai cin su ake yi.

Saboda yadda kiwata kaji na ci ba ya daukar lokaci kamar na masu yin ƙwai, sai nan da nan kasuwancin ya habaka.

Aiki a yanayin kasuwanci mai sauyawa ma ya taimaka sosai.

"Dole ne na yaba wa mahukunta bisa yadda suka saukaka min, saboda sun san cewa wannan kasuwancin zai samar da ayyukan yi da yawa, musamman ma ga matasan yankin.

Wannan gidan gona na biyan bukatar yankin, musamman ma kajin da ake ci. A lokacin da aka samar da isassun kaji, farashin na zama a yadda yake," mai sana'ar ya fada wa TRT Afrika.

Cikin nasara gidan gonar Michel Christophe bai samu wata illa ba daga ambaliyar ruwan da aka yi kwanan nan.

"Gidan gonarmu na ci gaba sosai. Kasancewar sa a kan tsauni, mamakon ruwan sama bai yi mana wata illa ba," in ji shi.

"Tun da farashi ya tashi zuwa yanayin da jama'a ke gwagwarmaya, akwai dama gare mu ta biyan bukatun jama'a a farashi mai sauki."

Samar da ayyukan yi

Michel Christophe ya dauki 'yan kasar rwanda su goma aiki don kula da gidan gonar.

Ma'aikatan sun hada da masu rainon kaji biyar, likitan dabbobi, da wasu ma'aikata ba na din-din-din ba.

Suna kula da lafiyar da lafiyar kajin, ba su abinci da tabbatar da ba su samu wata matsala ba.

Michel Christophe ya taimaka wajen cike gibin da ake da shi na kajin ci. Hoto: Mbadinga

Game da kayan aiki, gidan gonar na da kwanukan shan ruwan kaji 500 da kuma na cin abinci da dama.

Sannan yana da manyan tankuna uku da ke dauke da ruwa lita 5,000 da ake amfani da su kullum don samar da kaji 15,000 a duk kwanaki uku.

Bayan watanni na yin figar kaji da hannu, a yanzu gidan gonar Kazar Kauye ya samu injinan figa na zamani. Gonar na da manufar samar da kaji 30,000 nan da karshen shekara.

Duk wannan kokari da zuba jari da ake yi na shiga cikin farashin kajin.

Ana sayar da kajin da ake fitarwa daga gidan gonar kan kudin CFA 2,500 zuwa 3,000 ($4.2 zuwa $4.6) kowanne kilo daya. "Ina samar da kajin ne don sayarwa, na cike gibin da ake da shi a kasuwannin kasa.

A yanzu kuma na fara fitar da kajin zuwa kasashe irin su Congo-Kinsasha, inda na ke aika wa tan da yawa na kajin," in ji Michel Christophe yayin zanta wa da TRT Afrika.

A lokacin bukukuwa irin su Kirsimeti ne gidan gonar Kazar Kauye ya fi samun ciniki sosai.

Michel Christophe ya fahimci cewa kasuwanci ne da ke da kalubale, wanda ke bukatar hakuri, aiki tukuru da nutsuwa wajen kula da gidan gonar.

A kiwon kaji, 'yar karamar kwayar cuta sai ta janyo annobar tsuntsaye, wadda za ta janyo yaduwar cututtuka cikin sauri.

Gidan gonar Kazar Kauye ya yi ta kokarin kauce wa irin wadannan matsaloli, madalla da falsafar Michel Christophe na zama mai tsayin daka a ka'idojin kula da gidan gonar.

TRT Afrika