Yawancin kwantenonin da ake kai wa zuwa Nijeriya suna shigowa ne ta gabar ruwan Legas: / Hoto: Getty Images

Daga Abdulwasiu Hassan

Chidi Ebere, wani dan kasuwa ne a Nijeriya, wanda ba shi da damuwa kan kayan da ya yi oda daga Indiya, waɗanda suka taho ta teku kan hanyarsu ta zuwa Nijeriya. Babbar damuwarsa ita ce tashin farashin dauko kaya daga Legas zuwa kamfaninsa da ke Abia.

Ya fada wa TRT Afrika cewa, "Bambanci a kudin jigilar kaya daga Mumbai a Indiya zuwa Legas, da kuma bayan nan, zuwa birnin Abia a kudu maso gabashin Nijeriya yana da yawa. Akwai takaici a ce sai ka biya kudin jigilar cikin gida sama da na waje."

Nisan Mumbai a Indiya zuwa Legas a Nijeriya ta ruwa ya kai kilomita15,504, yayin da nisan Legas zuwa Abia kilomita 586 ne kacal. Amma me ya sa safarar kaya daga Mumbai zuwa Legas ya fi daga Legas zuwa Abia, duk da cewa ya ninka a nisa sau 26?

Ebere ya ce safarar kaya a cikin Nijeriya ta zamar masa abin tararrabi a kasuwancinsa. "Za ka dauki hayar motar kaya a Apapa (Legas) don daukar maka kaya a kwantena daga bakin ruwa, amma sai su caje ka akalla Naira 300,000 (dalar Amurka $399)".

"Wannan na faruwa ne saboda babu tituna masu kyau. Yana daukar akalla sati guda kafin motar ta kai ga daukar kwantenar." Har yanzu Ebere yana bukatar kashe kusan Naira 400,000, don tura kayan zuwa yankin kudu maso gabashin kasar, inda ofis dinsa yake.

Matsalar jigilar kaya tana da mummunan tasiri ga tattalin arziki. / Photo: Getty Images

Ya kara da cewa, "Kenan, ana kashe kusan Naira miliyan daya kan kwantena daga gabar ruwan Apapa zuwa Abia. Idan kana da kwatanta, ana kashe Naira 800,000 don kawo kwantena daga Mumbai zuwa Apapa a Legas".

Ebere daya ne daga cikin 'yan kasuwan Nijeriya da suke fama da irin wannan kalubale wajen jigilar kaya a kasar.

Shi ma Soremekun Rotimi Joseph, wani mai shigo da kaya da ke kasuwancinsa a Legas, ya ce yana kashe dala $350 don kai kwantena mai girman kafa-40, zuwa cibiyar kasuwancinsa a birnin.

Baya ga kudin jigilar kaya a cikin Legas, akwai jinkiri wajen fitar da kaya a wani yanayi na "karancin daidaito tsakanin kwastoma, da ma'aikatan tashar ruwa, da kamfanin safarar kaya", wanda yake shafar kasuwancinmu.

Wasu na fatan amfani da jirgin kasa don jigilar kaya a Nijeriya a wasu yankunan jihar Legas, amma wasu suna shakkar cigaban. / Hoto: Getty Images

Mafita a harkar jirgin kasa

Daya daga cikin dalilan da gwamnatin Nijeriya take kokarin daukaka amfani da jirgin kasa don jigilar kaya daga Legas zuwa yankunan cikin kasar, shi ne don rage kudin jigila.

Ministan sufurin Nijeriya, Sa'idu Ahmed Alkali, kwanan nan ya sanar da cewa an kusa fara amfani da jirgin kasa don jigilar kaya daga birnin kasuwanci na Kano – inda shi ma wata cibiyar kasuwanci ce a arewacin kasar.

Layin dogo da Turawan Burtaniya suka gina sun yi amfani a baya, lokacin da 'yan mulkin mallaka suka fahimci alfanun hakan. Wannan ya sa Nijeriya ta fara gina layin dogo na zamani, daga Legas zuwa Kano a shekarar 2017.

Layin dogon na zamani yanzu yana aiki daga Legas zuwa Ibadan. Ministan sufurin ya ce an gyara tsohon layin dogo daga Legas zuwa Kano. Kuma gwamnati za ta sayo taragon jirgi don daukar kwantena daga Apapa zuwa Kano.

Ba sabon abu be na

Masu ruwa da tsaki a harkar sufuri ba sa ganin wani kokarin gwamnati, inda suke nuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da ake batun amfani da jiragen kasa don jigilar kwantena ba.

Yayin da wani sashen titunan Legas suka lalace, ana samun jerin gwanon motoci masu dauke da kwantena kamar a wannan hoton na 2019. / Hoto: Getty Images

"A yanzu dai sanarwa ce kawai", in ji Mukhtar Danasabe Yusuf, wani mai aikin fiton kaya da ya zanta da TRT Afrika.

Ni dai zan jira sai na ga an kammala shirya "dabaru da tsarin wannan aikin" kafin na saka wani babban buri.

Shi ma Ebere yana da irin ra'ayin. Ya yi tambaya, "Mu dauka idan kana son aika kayan gwari, muna da wuraren ajiya a Apapa ne kawai. To, ta yaya tsarin zai yi aiki a Ibadan?"

Kayan gwari suna saurin lalacewa a yanayin rashin lantarki na tsawon lokaci, ko da a suto din tashar ruwa. Ebere ya ce, "Ko ma dai mene ne, wuraren ajiyar a tashar ruwan kawai ake da su. Kenan, ina ganin idan aka ce an gina tsarin da ya wuce wannan, bayan babu komai a kasa, to duka magana ce kawai".

Yayin da 'yan kasuwa suke dakon gwamnati ta kammala shirin amfani da jirgin kasa don jigila, Mukhtar ya yi amanna cewa jigilar kaya ta amfani da titi ita ce kawai hanyar da masu harkar suke da ita.

Ya kara da cewa, "Idan kana son zuwa kowace tasha a arewacin Nijeriya ta titi, zai dauke ka akalla kwana hudu zuwa biyar, saboda yanayin da tituna suke ciki".

Kalubalen fiton kaya

Tarin masu matsakaicin arziki a Nijeriya suna hijra don neman damarmaki a kasashen waje, wanda ke janyo yawaitar neman kayan abinci irin na gida a kasashen waje, saboda 'yan kasa da ke kwadayin abincin gida.

Mukhtar ya ce, "Karuwar kayan da ake fita da su daga Nijeriya ya kai matakin irin na kayan da ake shigowa da su daga Indiya, ko China, ko Turkiyya, ko Amurka. Wannan ya faru ne saboda karuwar 'yan Nijeriya da ke komawa kasashen waje da zama".

Wasu 'yan Nijeriya suna ganin kasar tana bukatar amfani da sauran tashoshin ruwanta kamar na Onne a jihar Rivers. / Hoto: Getty Images

Akwai tarin gudunmawar da harkokin fiton kaya suke bayarwa ga tattalin arziki, ko da kuwa akwai matsalolin jigilar.

Masu aikin fiton kaya, kamar su Mukhtar sun ce tsawon lokacin da ake bukata don kammala aikin fiton kaya yana da karya gwiwa, kuma yana da tsada.

Ya ce, "Haka nan, yanayin da tituna ke ciki daga arewacin kasar zuwa tashoshin bakin teku suna bukatar gyara kafin harkar kasuwanci ta yi sauki".

Masu fitar da kaya da masu shigo da kaya suna fatan gwamnati za ta samo hanyar shawo kan wadannan kalubale na jigilar kaya, ta yadda 'yan kasuwar cikin gida za su iya samun damarmaki da suka shafi kasuwanci mara haraji.

TRT Afrika