Daga Firmain Eric Mbadinga
Binta Keita, mai kula da yara a Dakar, na da wayar Android wadda ba ta iya amfani da ita yadda ya dace saboda rashin iya sarrafa fasahar zamani da aka samar da wayar da ita.
Ko da dan karamin abu irin yin saka kudi a waya, tana fita waje neman wanda zai taimaka mata duk da kuwa tana da manhaja a kan wayarta da aka tsara don yin hakan.
"Rashin sanin rubutu da karatu, ba ni da zabi da ya wuce na je ko ma ina ne don neman taimakon" Binta, wadda ke da shekaru talatin da dan wani abu ta fada wa TRT Afrika.
Ba ita kadai ba ce aka bari a baya a gogayyar samun saukin rayuwa da ake yi ta hanyar rungumar fasahar zamani.
A Sanagal, ana kiyasta sanin rubutu da karatu da kashi 42 a tsakanin jama'ar da suke su miliyan 16.
Wadannan alkaluma na bayyana cewa kusan mutane miliyan tara ba su iya rubutu da karatu ba, duk da cewa hakan bai fitar da su daga da'irar zama wani bangare na rayuwar kasar ta Sanagal.
To, ta yaya mutane irin su Binta suka zama wani bangare na tattalin arziki da ke bukatar 'yan kasa da ba su iya rubutu da karatu ba su zama sun iya amfani da yanar gizo kamar biyan kudade ko yin sayayya?
Wani kamfanin Senagal mai suna Andakia ya dauki matakin kubutar da Binta a miliyoyin 'yan kasar irin ta daga duhun rashin iya amfani da abubuwan da za su saukaka musu rayuwa.
Kirkirarriyar Basira ga kowa
AWA, tsarin kirkirarriyar basira da ke magana da harshen Wolof da Andakia ya samar, tsari ne da Alioune Badara Mbengue ya kirkira.
Wannan matashi dan Senagal mai sha'war kirkirar sabbin abubuwa ne da ya kware a fannin kirkirarriyar basira (KB) da kirkire-kiren zamani.
Tare da Andakia, Alioune da abokan aikinsa sun yi alkawarin bai wa KB siffar Afirka.
"Burinmu shi ne mu samar da yanayin da du wani dan Afrika zai iya amfani da cigaban zamani ta hanyar kawar da matsalar yare," ya fada wa TRt Afrika.
"A 2015, mun hada hannu wjen kirkirar Mbal-it, kwandon sharar yanar gizo, wanda ke bayyana mana cewa fasahar zamani ta kere-kere na bukatar yin magana da yarukan kasa don ganin kowa ya rungume ta."
Tawagar ma'aikatan Andakia sun dauki wasu shekaru suna habaka wa da samar da mafita wand ahakan ya kai ga kaddamar da fara amfani da AWA a 2024.
Alioune ya kara da cewa "Da farko dai AWA Kirkirarriya Basira ne da ke fahimta da magana da harshen Wolof.
Manufarmu ita ce a shigar da AWA zuwa sauran yarukan Afirka, don mayar da Afirka jagora a kirkire-kirkiren sadarwar zamani ta dijital da kuma karfin fasahar kere-kere da ke biyan bukatunta."
Tun bayan bayyana fitar da aikin AWA ta hanyar bidiyo a shafukan sada zumunta, sai kawai aaka dinga ganin nuna sha'awar amfani da shi a Dakar da ma wasu garuruwan.
Abdoul Toure, wani mai shago a unguwar Medina da ke babban birnin Sanagal, na daga cikin wadanda ke sauraren fara amfani da manhajar a wayarsu.
"Na fara samun labari game da wannan daga dan'uwana Alassane. Ya san abubuwa da yawa game da fasahar zamani, amma ban yarda da su ba saboda wadannan abubuwa ne da ne ke gani a fina-finai."
Abinda ya sauya ra'ayin Abdoul shi ne ganin wadanda suka kirkiri wannan KB din na gabatar da aikinsa a talabijin.
"Abu ne mai kayatarwa na fasaha, ina sauraren amfani da shi," in ji shi.
Kamar Binta, mai sayar da kayan marmarin na fatan samun 'yanci sosai a lokacin da ya zo amfani da fasahar ko yanar gizo.
Yana bayyana damuwa game da ko bayanansa musamman na hada-hadar kudi za su iya fuskantar hatsarin fada wa hannayen wasu a lokacin da ya nemi taimakon wani wanda a dan'uwansa ba, musamman wajen kashe kudi ko sayen wani abu ta yanar gizo.
Kwararru kan fannonin kafafen sadarwa da dama Melba Orlie, Ibrahima Khalil Ba, Pape Gorgui Ndoye, Mandiaye Gningue da Tidjane Tall, wadanda dukkan su sun shiga aikin, suna kara fahimtar irin rawar da AWA zai taka a rayuwar jama'a.
A wajen kowanne mamba na wannan kamfani, suna kallon aikin a matsayin wani nauyi da kuma zama abin alfahari inda suka dauki nauyin aikin da zimmar ganin ya tabbata don inganta rayuwa.
Tawagar matasa ta Andakia ta zama irin ta Injiniyoyin Kirkirarriyar basira (KB), masu habaka wa, kwararru kan UX/UI, masu basira, kwararru kasuwanci da tallata shi da kuma masu sarrafa harshe.
"Cikin tsanaki mun tattara kwararru waje guda daga fannoni daban-daban don gina tawagar da za ta iya tunkarar duk wani kalubale ami rikitarwa da samar da mafita kowace iri ga wannan aiki," Alioune ya shaida wa TRT Afrika.
Yadda AWA ke aiki
Andakia, wanda ya tabbatar da mutane 200 sun sun gwada aiki da AWA a kwanaki da dama, ya samar da shirin ta yanar gizo da manhajar wayoyin hannu.
Za a iya shigar da shi cikin manhajoji irin su Whatsap ko manhajojin API don gudanar da kasuwanci.
Andakia na kuma yin shirin aiki da ma'aikatun gwamnati don a samu a amince da rungumar AWA.
Masu amfani da AWA na bukatar yin magana ne da fasahar ta Kirkirarriyar Basira (KB) da yaren Wolof, suna neman wasu bayanai na bai daya ko tambayar wani abu kamar kiran motar tasi, sayen abinci, ko yin mu'amalar kudi.
Ga masu habaka fasahar Sadarwar Zamani, AWA wata saha ce da za ta bayar da damar shigar da ita kai tsaye cikin manhajojinsu.
"Wannan na nufin cewa wasu manhajojin yanar gizo da suka takaita ga yarukan Faransanci da Turancin Ingilishi za su bayar da ayyuka a yarukan cikin gida na Afirka misali shi ne yaren Wolof," in ji Alioune.
Misali, bangaren kula da masu amfani na Whatsapp zai amsa tamboyoyin masu amfani da shi a harshen Wolof a cikin yanayin na gaske d ayadda yaren yake aiki, wanda zai kawo sauki ga miliyoyin mutane wajen samun hidindimu daban-daban da suke bukata.
"Wadannan ayyuka za su samar da mafita ga ayyukan jama'a na yau da kullum, kuma manhajar AWA za ta biyo baya wajen bayar da dama ta kai tsaye ga daidaikun mutane." Alioune ya shaida wa TRT Afrika.
Andakia na tabbatarwa masu amfani cewa za a kare bayanansu a waje mai tsaro, wanda suke aiki da dokoki da tabbatar da fifikon manhajar sama da komai.
Samo asali daga addini
Manhajar AWA ta samo sunansa ne daga Hawwa, ma'ana Hauwa'u a harshen Larabci, matar mutum na farko da aka halitta, Annabi Adam (AS).
Sabanin sautin da ake samarwa ta hanyar amfani da KB, muryar AWA ta zama sai ka ce ta dan adam sosai, hawa da saukar sauti, musamman karin sautin Sanagal.
"Mun hada hannu da karfe da kwararru kan yaruka da masu magana da yaren na asali don koya wa matanin yadda zai karanta.
Wannan ya tabbatar da dadai, furuci daidaitacce a Wolof a lokacin da yake kuma aiki da ka'idojin al'adu," in ji Melba Orlie, mace kwaya daya da ke cikin tawagar Andakia.
Tun 1 ga Nuwamban 2024 masu amfani suka fara aiki da AWA, wanda aka nuna a wajen taron kaddamar da manufofin Sanagal na 2050, inda ta bayyana a cikin yaren Wolof muhimmanci da ginshikan shirin a yayin da Firaminista Ousmane Sonko ke gabatar da jawabi.
Duk da cewa AWA na magana ne sosai a yaren Wolof, wadand asuka kirkiri wannan abu na ta kokarin ganin sun fadada yarukan ta yadda al'ummu da dama za su shigo cikin shirin nasu.
Tare da sauran manyan yarukan Sanagal irin su Pulaar da Hausa, AWA zai samu yaruka da dama a kan sa.
Game da muryar mace kuma, Alioune ya tabbatar da cewa hakan zai zama muryar shirin nasu.
"AWA za ta zama AWA a koyaushe. Tuni masu amfani suka mayar da manhajar tasu. Ya zama ruwan dare yadda mutane ke kiran mu da ina AWA idan sun gan mu a hanya.
Wannan shaida ce da ke nuna murya da sunan AWA sun zauna a bakunan mutane kuma suna jin dadin amfani da su," in ji shi.
A yanzu Andakia na aiki kan manhajojin da suka shafi fannonin lafiya, ilimi, da ayyukan noma don samar da mafita da yin tasiri mai karfi ga al'umma.