Daga Firmain Eric Mbadinga
A 2014 rayuwar Alain Bilas ta samu gagarumin sauyi - ya rasa aikinsa, kuma wani abu mafi muni, abokiyar zaman sa ta kaurace masa.
Sakamakon gaza jure wadannan musibu guda biyu, matashin dan kasar Kamaru ya yi kokarin kashe kansa.
Amma kaddara ta riga fata. Masoyan Alain sun shiga tsakani a lokacin da ya dace inda suka kubutar da rayuwarsa ta hanyar kawar da mummunan zato da yanke kauna da suka kusa halakar da shi.
Wani abokoinsa bai samu wannan nasara ba. Shekaru biyar bayan Alain ya dawo daga rakiyar kashe kai, abokinsa ya kashe kansa saboda matarsa ta gudu ta bar shi.
Zafin rasa wani da yake kusa da shi saboda wani yanayi da ya taba samun kansa a ciki ne ya sanya Alain zama cikakken mai yaki da yunkurin kashe kai.
Tsakanin sana'arsa, kula da iyali da ayyukan yau da kullum, wannan malamin makaranta da ya fito daga yankin Bertoua na gabashin Kamaru ya samu damar cika burinsa na yaki da abinda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana a matsayin fifikon lafiyar jama'a a nahiyar.
WHO ta bayar da rahoton cewa mutane 11 daga cikin 100,000 a Afirka na mutuwa ta hanyar kashe kai.
Inda kiyasin ya nuna a duniya baki daya mutane 726,000 ne ke mutu sakamakon kashe kai a kowace shekara.
"Na taba fuskantar rashin kyauta a wjaen sana'a. Idan har hakan ba shi da muni sosai, a wannan lokacin abokiyar zamana ta guje ni.
"Wannan ne ya sanya ni fara tunanin kawo karshen rayuwata," Alain ya fada wa TRT Afrika wannan yanayi mafi muni a rayuwarsa.
Gano cewar mutuwarsa z ata janyo rashin jin dadi ga masoyansa ya karfafa gwiwar Alain na gyara rayuwarsa.
Wani babban abu shi ne yadda yake iya bude baki ya yi magana game da lamarin da ake yi wa kallon wani babban abin kunya a tsakanin wasu al'ummun.
Taimako nan da nan
Ayyukan Alain, Kungiyar Yaki da Kashe Kai ta Kamaru, na ayyuka a dukkan fadin kasar, ciki har da babban birnin Yaounde, Douala, Kribi, Garoua da Maroua.
Kungiyar ta samar da wani tsari d amambobinta ke aiki a kai, wanda adadinsu ke daduwa a koyaushe tun bayan kaddamar da kungiyar.
Mafi yawancinsu sun taba kokarin su kashe kawunansu a lokacin da rayuwa ta yi zafi ko idan suka rasa wani masoyinsu.
Domin yaki da wannan ta'ada a aikace da smaun tasiri mai kyau, kungiyar Alain ta mayar da hankali wajen wayar da kan jama'a ta hanyar mu'amalantar su, gangami, da ma ta shafukan sada zumunta.
Gangamin na amfani da dabaru na gargajiya irin su zuwa bakin kofofi da gidajen mutane da bayyana talabijin da rediyo.
Kungiyar tana kuma amfani da sabbin hanyoyin sanyaya gwiwa da kawar da tunanin masu kokarin kashe kawunansu, inda kwararru suka bayyana a matsayin ciwon kwakwalwa.
WHO ta ce batutuwan da suka shafi zamantakewa, al'adu, iyali, kwakwalwa da muhalli ne ke janyo kashe kai.
Matsalolin tattalin arziki ma na kara janyo wannan matsala.
Baya ga rasa aiki da kuma guduwar abokiyar zaman sa, kamar dai yadda Alain ya fuskanta shekaru goma da suka gabata, damuwa ko matsalolin lafiya na iya kai mutane ga tunanin su kashe kansu.
Cibiyar Nazari Kan Cutar Kwakwalwa ta ce rashi ko mutuwar masoyi, guduwar masoyi su bar mutum, ko fuskantar barazana daga wasu makamai na iya jefa mutum cikin hatsarin tunanin kashe kai.
Fadawa tarkon nuna ƙyama
"Da zarar mun fara fita fili don tunkarar mutane, sai mu gano cewa akwai wata kullalliya da ke janyo wannan matsala ta kashe kai.
"Sai sakonmu ya zama, 'Mafita ga kashe kai shi ne a tattauna a kan ta'," Alain ya fada wa TRT Afrika.
"Tun bayan mun fara wannan, za mu iya cewa mutane da dama na ta tutubar mu don taimaka musu fita daga kangin tunanin da suka shiga."
Dabarar sadarwar ta yi aiki da amfani a matakai da dama, ciki har da daina nuna kyamata ga wadanda ke da wannan tunani, sannan sai taimakon daidaita tunani da kwakwalwa duba ga matsalar mutum.
Wani labari da ya karfafa gwiwar kungiyar ta Kamaru shi ne na wani matashi wanda ya rasa ta yadda ya rasa yadda zai biya mahaifiyarsa kudinta bayan ta ba shi ya amfani da su a cacar wasanni.
A lokacin da yake gaf da kashe kansa, mambobin kungiyar sun sanya shi ya bayyana kuskurensa ga mahaifiyarsa, tare da neman yafiyarta wanda mataki ne marar illa.
Wannan ya sanya shi fahimtar cewa mahaifiyar sa za ta fi yi bakin ciki idan ta rasa shi gaba daya, idan aka kwatanta da bakin cikin da take ciki bayan ta gano ya yi asarar kudade da yawa a caca.
"Abun takaici ga kowa, mun hadu da shi ta shafin sada zumunta a wannan bakin yanayi na rayuwa.
"Yana da karfin gwiwar tuntubar mu, madalla, taimakonmu ya haifar da da mai ido, kuma yau ya yi digirgir, ya yi aure, yana zaune da iyalansa," in ji Alain.
Hadin kan kasa
Kamar yadda yake a shekarun da suka gabata, manufar kungiyar a 2024 ita ce a roki mahukunta da sauran abokan aiki da su samar da wani tsari na kasa don hana afkuwar kashe kai.
A tsawon shekara, kungiyar ta ziyarci manyan makarantu, jami'o'i, da sauran wuraren taruwar jama'a don karfafa musu gwiwar aiki a bayyane da tattaunawa don kawar da matsalilin da ke ingiza mutane su yi yunkurin kashe kawunansu.
A kowace ranar 10 ga Satumba, Alain da sauran mambobi na shirya taruka don Bikin Ranar Yaki da Kashe Kai ta Duniya.
A ranar Lahadi ta uku kowane watan Nuwamba, kungiyar na shiga Bikin Ranar Bakin Ciki Kan Kashe Kai ta Duniya.
Kungiyar Kasa da Kasa Mai Yaki da Kashe Kai na tallafa wa Alain da abokan aikinsa.
A matakin kasa, kungiyar na neman taimako da goyon bayan ma'aikatun lafiya da ilimi, wadanda dukkan su na taimaka wa wajen gudanar da ayyuka da shigar jama'a cikin shirin.