Akwai yuwuwar karuwar cututtuka masu alaƙa da gurɓataccen abinci. / Hoto: Reuters  

Daga Dayo Yussuf

Yayin da mutane kusan mutum miliyan guda suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa na baya-bayan nan a yankin gabashin Afirka, hukumomi a kasashe daban-daban na fargabar cewa akwai yiwuwar cututtuka da ake ɗauka cikin ruwa su iya kara janyo asarar rayuka a yankunan da ya lamarin ya fi kamari.

Akalla mutane 300 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a kasar Kenya kadai, yayin da wasu daruruwa kuma suka jikkata, kana kusan mutane rabin miliyan suka rasa mastugunansu a kasar.

Hukumomin kasar sun bayyana damuwarsu game da illolin kiwon lafiya la'akari da mutanen da ke amfani da gurbataccen ruwan ambaliyar sakamakon rashin samun samun ruwa mai tsafta.

''Akwai yiwuwar kamuwa da cututtukan da ke da alaƙa da gurɓataccen abinci," a cewar Abdourahmane Diallo, wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya WHO a Kenya.

Gwamnatin Kenya ta ce ambaliyar ruwan ta lalata muhimman ababen more rayuwa tare da mamaye hanyoyin magudanar ruwa na birane.

An rufe wasu cibiyoyin kiwon lafiya 14 a fadin kasar sannan an samu gurbacewar ruwa na wata babbar tashar ruwa sakamakon ambaliyar.

Masana sun yi gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a fara samu yaduwar cututtuka da ake ɗauka daga cikin ruwa idan har ba a ɗauki matakai kuma an yi taka-tsantsan ba.

Masu bincike sun yi kiyasin cewa a duk shekara akwai mutane miliyan 1.3 zuwa 4.0 da ke kamuwa da cutar kwalara, sannan mutane 21,000 zuwa 143,000 ne suke mutuwa a duniya sakamakon cutar kwalara. / Hoto: Reuters

''Dole mu kasance masu sa ido sannan a shriye wajen bin matakai, karkashin jagorancin gwamnati da kuma abokan hulda, don kawo dauki ga daruruwan da dubban mutanen da lamarin ya shafa,'' in ji Mista Diallo a yayin gargadin da ya yi a Nairobi babban birnin kasar Kenya.

Akalla mutane 50 ne aka rawaito sun kamu da cutar kwalara a Kenya tun daga lokacin ambaliyar, yayin da wasu daruruwan mutane kuma suke fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka masu alaƙa.

Muhimman bayanai game da Kwalara: (WHO)

• Kwalara, cutar amai da gudawa ce da ake saurin kamuwa da ita, sannan tana iya kisa cikin sa'o'i kadan idan ba a yi maganinta ba.

• Masu bincike sun kiyasta cewa a kowace shekara ana samun mutane miliyan 1.3 zuwa 4.0 da ke kamuwa da cutar kwalara, sannan mutane 21,000 zuwa 143,000 ne ke mutuwa a duniya saboda cutar.

• Kusan kashi 10 cikin 100 na tsananin alamun cutar sun hada da gudawa da kuma ƙaracin ruwa a jikin mutum.

• Tsananin yanayin cutar na buƙatar maganin gaggawa tare da sanya ruwa zuwa jikin mara lafiya da maganin kashe ƙwayoyin cuta na Antibiotics.

• Samar da tsaftataccen ruwan sha da muhalli, da kuma yanayi tsaftatacce ma na da matukar muhimmanci wajen hana kamuwa da cutar kwalara da sauran cututtuka da masu yaduwa da ake ɗauka daga cikin ruwa.

• Akwai buƙatar a yi amfani da rigakafin cutar kwalara na ruwa tare da tsaftace ruwan sha da kuma muhalli don takaita barkewar cutar da kuma rigakafinta a wuraren da ake da barazanar daukar cutar ta kwalara.

Hukumar Lafiya ta Duniya  WHO tana kan ƙira ga mutane da su kaurace wa wuraren da abin ya shafa don gujewa kamuwa da cututtuka kamar kwalara da typhoid / Photo: Reuters

Sauran cututtukan da za a iya kamuwa da su ta hanyar shan gurɓataccen ruwa ko abinci sun haɗa da cutar Hanta ta Hepatitis-A da typhoid da dysentry da ke janyo ciwon ciki, sai kuma cutar shigellosis da ke iya yaduwa ta hanyar saduwa da mai cutar.

Alamomin cututtukan sun hada da zazzabi, da kasala da tashin zuciya da amai da gudawa da rashin jin dadin ciki da shawara (jaundice) da kuma fitsari mai duhu.

Hukumar ta WHO ta bukaci mutanen da ke zaune a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa da su tabbatar da sun samar da tsaro a abincnsu ta hanyar dafa abinci yadda ya kamata da kuma inganta hanyoyin aijiya da kuma tsaftace baƙi daya.

Sai dai haɗuran kiwon lafiya a waɗannan lokuta sun wuce iya abin da za a saka a baki kawai, kazalika kewayen mutum na iya janyo cututtuka.

Masana sun yi gargadin cewa kaurar mutane da cunkoso a matsugunai da sansanonin na iya haifar da yaduwar cututtuka waɗanda ka iya janyo cutar da ta shafi numfashi.

Akwai cututtukan da suke yaduwa ta hanyar cizon dabbobi da kwari waɗanda ake ganin suna bunƙasa ta wannan yanayin. Hoto: Reuters

Mafi yawan cututtuka na numfashi da ake ɗauka a lokutan ambaliya sun haɗa da cutar mashako da Asma da cututtukar da suka shafi huhu da mura mai tsanani.

Ana saurin ɗaukar Ire-iren waɗannan cututtuka ko kuma a yaɗa su daga wani mutum zuwa wani musamman a wuraren da babu iska sosai ko kuma cikin cunkoso.

A cewar hukumomin kasar Kenya, kananan hukumomi 41 ne daga cikin 47 ambaliyar ruwan ta shafa, lamarin da ya sa dubun dubatar mutane suka yi gudun hijira zuwa yankunan da suka fi tsaro.

Mafi yawancinsu mutanen suna neman mafaka ne a cikin makarantu da majami'u.

Kazalika akwai haɗuran ɗaukar cututtuka da galibi ke yaduwa ta hanyar cudanya da dabbobi da kwarin da ake ganin suna bunƙasa a irin wannan yanayi, a cewar gargadin da masana suka yi.

Cututtukan sun hada da zazzabin cizon sauro, da zazzabin Rift Valley, da zazzabin West Nile da kuma Leptospirosis.

Ana iya danganta cututtukan a matsayin masu alaƙa da bala'o'i ko iftila'in ambaliya.

Sannan ana kamuwa da cututtukan ne ta hanyar cizon sauro, manya bera da dabbobin da ake kiwo a gida.

Alamomin farko sun hada da yawan zazzabi da gumi da rawar sanyi da ciwon kai da na gabobi da ƙin cin abinci da tashin zuciya da amai.

Sai dai masana sun kuma yi wa iyaye gargadi da cewa su sa ido sosai kan wasu alamomi ko mastaloli da ke tattare da kwakwalwar 'ya'yansu a yayin ko kuma bayan wucewar iftila'in ambaliyar ruwan sama.

A cewar kungiyar agaji ta Red Cross a Kenya, hotunan barna, da rushewar gidaje da ababen more rayuwa har ma da mace-macen da aka samu sakamakon ambaliyar na iya yin tasiri na dogon zango kan yara.

"A yayin wani iftila'i kamar abin da kasarmu ta fuskanta, yara kan faɗa cikin wani yanayi na tsaro da firgici da kuma damuwa," a cewar wani sako da Kungiyar Red Cross ta Kenya ta wallafa a shafinta na X.

''Shawarwari na taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa yaran tare da kara musu fahimtar yanayin da ake ciki da kyau,'' in ji Red Cross.

Ma'aikatar hasashen yanayi ta Kenya ta yi hasashen za a ci gaba da samun ruwan sama a makonni masu zuwa, lamarin da ke kara barazana ga rayuka da cututtuka da ake ɗauka saga cikin ruwa.

Sai dai lamarin ba a iya Kenya kadai ya tsaya ba.

Masana sun gargadi iyaye da su kula da lafiyar kwakwalwar ’ya’yansu a yayin ko bayan iftila'in ambaliyar ruwa. / Hoto: Reuters

Kimanin mutane miliyan daya ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kasashen Burundi da Kenya da Rwanda da Somaliya da Habasha da kuma Tanzania, a cewar Ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya, ya kuma kara da da cewa adadin na karuwa yayin da ruwan sama ke kara kamari.

Don haka yayin da mutane ke kiyayewa a lokutan ambaliya, masana sun ba da shawarar cewa akwai buƙatar a zauna cikin shiri sosai don tunkarar abin da ka iya zuwa a gaba wanda illa ko tasirinsa na iya muni sosai.

TRT Afrika