Bangaren auduga na daukar ma'aikata kusan miliyan 20 a kasashe hudu da suka hada da Burkina Faso, Mali, Benin da Chadi. Hoto: Reuters  

Ƙasashen Afirka da ke noman auduga sun yi kira ga hukumar kasuwanci ta duniya WTO, da ta samar da mafita kan “karkatar da kasuwancin auduga” da manyan ƙasashe masu masana’antu ke haifarwa.

Kiran nasu ya zo ne gabanin Taron Ministocin Ƙungiyar WTO da za a buɗe a birnin Abu Dhabi a ranar Litinin.

Ƙasashen waɗanda ake musu laƙabi da C4, wato ƙasar Jamhriyar Benin da Burkina Faso da Mali da kuma Chadi - sun yi kira da a kawo ƙarshen tallafin auduga ga ƙasashe kamar Amurka da Indiya da China, inda suka ce yin hakan yana tasiri kan farashin audugar cikin gida.

''A shekaru 20 da suka wuce, tsaikon da aka haifar a cinikayyar auduga na ci gaba da yin illa ga rayuwar milliyoyin masu noman auduga a ƙasashen C4 na Afirka,'' kamar yadda Ministan Masana'antu da Kasuwanci na ƙasar Chadi Ahmat Abdelkerim ya shaida wa taron manema labarai a ranar Lahadi a birnin Abu Dhabi.

'Babbar gudunmawa'

Ƙasashen C4 sun kuma yi kira kan a biya su diyya ga ɓarnar da aka yi ya zuwa yanzu, tare da cire batun auduga daga kundin aikin gona don ciyar da tattaunawa gaba.

Wasu manoma a gonar auduga na Korhogo da ke Ivory Coast Nuwamba 21, 2023. REUTERS/ Media Coulibaly

Cote d'Ivoire da kasashen C4 sun gabatar da daftarin ƙuduri kan auduga ga Hukumar Kasuwanci ta Duniya a shirye-shiryen taron hukumar da za a yi a Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda za a fara a ranar Litinin.

Sai dai Ministan na Chadi ya ce "ba a yi la'akari da shawarar daftarin ba," duk da cewa auduga tana da mahimmanci "ba kawai ga samar da ayyukan yi ba, har ma da samar da abinci".

"Za ta ba da gudunmawa sosai ga zaman lafiya" a Afirka, in ji shi.

Ɓangaren auduga na da ma'aikata sama da miliyan 20 a ƙasashen C4, kuma darajarsa ya kai dala biliyan biyu, a cewar Ibrahim Malloum, wakilin ƙasar Chadi da ke kula da harkokin kasuwanci.

Darajar cinikayyar auduga

"Batu ne kan samar da daidaito da kuma daidaita tattalin arziki," in ji Ministan Masana'antu da Kasuwanci na Mali Moussa Alassane Diallo a wajen wani taron manema labarai.

Wasu Manoma suna aiki a gonar auduga a Korhogo, Ivory Coast Nuwamba 21, 2023. REUTERS/ Media Coulibaly

Darakta Janar ta Hukumar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala da shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA, Gianni Infantino sun sanar a ranar Asabar cewa, ƙungiyoyin biyu za su ƙarfafa haɗin gwiwarsu kan auduga, tare da yin kira da a taimaka wa ƙasashen Afirka wajen shiga cikin darajar cinikayyar auduga.

Akwai yiwuwar batun noma ya gaza kai labari a taron na WTO, la'akari da yadda ƙasashe da dama ke adawa da matakin da aka ɗauka don fargabar hakan ka iya kawo cikas ga kasuwannin abinci na duniya.

TRT Afrika