Nan da shekarar 2025 Turkiyya za ta fara fitar da motar da ta kera samfurin Togg mai aiki da lantarki zuwa kasashen ketare, in ji Shugaban Kasar Recep Tayyip Erdogan.
“Nan da 2025 za mu fitar da Togg tare da sayar wa da duniya,” in ji Shugaba Erdogan a wajen bukin kaddamar da cibiyar hada wa da samar da batiran SIRO a lardin Bursa.
Erdogan ya kara da cewar Turkiyya na da manufar samar da Togg guda miliyan daya nan da 2030.
“Tare da motarmu da muka samar a kan tituna, kasarmu ta mallaki mota da za ta yi gogayya da irin ta masu inganci a duniya,” a fadin Shugaba Erdigan inda ya kara da cewar kasashe kawayen Turkiyya sun bukaci a aika musu da motar.
A farkon watan Afrilun nan ne motar Togg ta fara yawo a kan tituna bayan an fara mika wa Shugaba Erdogan tasa da ya saya, wanda ya bayyana motar ta zama alamar cigaban fasahar kere-kere, tattaln arziki da kimar Turkiyya.
‘Cibiyar kere-kere
Game da sabon kamfanin kera batiran a yankin Gemlik na lardin Bursa, Erdogan ya ce a shekarar 2024 zai fara aiki gadan-gadan.
Erdogan ya kuma ce “Nan da 2026, wannan cibiya za ta zama ta bai daya wajen samar da ingantattun batira da ma kayayyakin hada su” inda ya kara da fadin wannan zuba jari zai sanya Turkiyya ta zama “babbar mai taka rawa” wajen fasahar samar da batira.
Shugaban ya jaddada cewa “Mun shirya tsaf don mayar da Turkiyya ta zama cibiyar kere-kere ta Turai a fannin caji da fasahar kera batira da ma ababen hawa masu aiki da lantarki.”