Erdogan: Mota kirar Turkiye mai aiki da lantarki za ta fara yawo a kan tituna

Erdogan: Mota kirar Turkiye mai aiki da lantarki za ta fara yawo a kan tituna

Turkiye ta samar da motar mai suna TOGG  da ke aiki da lantarki dari bisa dari.
TOGG / Photo: AA

Shugaban Kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa motar da aka jima ana jiran fitowar ta masi suna TOGG kirar Turkiye da ke aiki da lantarki za ta fara yawo a kan tituna a karshen wannan watan.

Ya ce, kusan mutane dubu tamanin ne suka bayar da kudade don sayen motar.

Shugaba Erdogan ya kara da cewa a tsakanin 16 da 27 ga Maris za a karbi bukatar sayen motar samfurin TOGG T10X daga wajen masu sha’awar saya.

Farashin matsakaiciyar motar TOGG T10X zai fara daga Lira 953,000 (Kusan dala 50,200) zuwa Lira miliyan 1,055,000 (kusan dala 55,600), haka kuma farashin doguwar motar TOGG zai kasance Lira miliyan 1,215,000 (Kusan dala 64,000).

Erdogan ya kara da cewa a wannan shekarar ana da manufar samar da TOGG guda 20,000.

Ya ce “Muna fatan samar da motocin TOGG miliyan daya nan 2030”.

AA