Erdogan ya ce an samu albarkatun man ne a zurfin mita 2,600 / Photo: AA

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da cewa sun gano karin albarkatun man fetur a gabashin kasar.

“Zan so na ba ku labari mai dadi. Mun gano danyen man fetur da a kowacce rana za a iya diban ganga 100,000 a Judi da Gabar,” in ji Shugaban a lokacin da yake kaddamar da aikin cibiyar makamashin rana da aka kammala a Karapinar da ke lardin Konya na tsakiyar kasar.

Da yake bayyana cewar man fetur din da aka samu a kusa da Sirnak na da inganci sosai, Erdogan ya jaddada cewa “Turkiyya ba za ta sake dogaro ga wasu kasashe ba don samun makamashi inda ta zama mai fitar da shi zuwa kasashen waje.”

Erdogan ya ce albarkatun man da aka samu a zurfin mita 2,600, za a fito da su ta hanyar amfani da rijiyoyi 100 kuma zai biya bukatar 1 bisa 10 na man fetur da Turkiyya ke da ita.

Erdogan ya ce an saka wa rijiyar man sunan matashiyar malamar koyar da kida Aybuke Yalcin, wadda ‘yan ta’addan PKK suka kashe a 2017 a wani harin ta’addanci a kudu maso-gabashin Turkiyya.

Yalcin, mai shekaru 22, ta rasu ne a harin da ya rutsa da ita wanda aka nufi motar shugaban yankin Kozluk a lardin Batman a ranar 9 ga Yunin 2017. Tana cikin wata karamar motar bas da ke tare da ayarin motocin shugaban.

Ya ce “Sunan sabuwar rijiyar manmu shi ne Shahidiya Aybuke Yalcin-1, kuma muna sa ran za a samu karin albarkatun mai a wannan yankin.”

Game da cibiyar Nukiliya ta Akkuyu, Shugaba Erdogan ya ce kasar za ta iya samun kashi 10 na makamashin da take bukata daga cibiyar, kuma akwai yiwuwar gina cibiyar Nukiliya ta biyu a Sinop.

Erdogan ya yi alkawarin kawar da ta’addanci daga dukkan batutuwan da suka shafi Turkiyya, kuma kasar za ta magance duk wani kalubale da ya hana ta amfana da arzikin da take da shi yadda ya kamata

Kungiyar ta’adda ta PKK da ta yi shekaru sama da 35 tana kai hare-haren ta’addanci, na jerin sunayen kungiyoyin da Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ‘yan ta’adda na kasa da kasa.

Ta kashe mutane sama 40,000 da suka hada da mata, yara kanana da jarirai.

TRT World