Sabon Karamin Ministan albarkatun man fetur na Nijeriya ya ce nan da karshen 2024 dukkan matatun fetur na kasar za su soma aiki.
Heineken Lokpobiri ya bayyana haka ne ranar Juma’a yana mai cewa matatar mai ta Fatakwal za ta soma aiki a watan Disamba mai zuwa.
A lokacin da yake duba ayyukan da ake yi a matatar man ta Fatakwal, ministan ya ce "daga abin da na gani a nan a yau, za a iya cewa matatar mai ta Fatakwal za ta soma aiki nan da karshen shekarar nan."
Ya kara da cewa sauran matatun mai da ke Warri da Kaduna za su soma aikin tace danyen mai daga watanni hudu na farko zuwa karshen 2024.
A baya, gwamnatin kasar ta ce matatar mai ta Fatakwal za ta soma aiki a karshen 2022.
Sai dai ministocin da suka hau mulki da kuma kamfanin man fetur na kasar NNPCL ba su cika wannan alkawari ba.
Amma Lokpobiri ya ce "burinmu shi ne... mu tabbatar nan da karshen shekara mai zuwa Nijeriya ta daina shigo da man fetur."