Fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da Turkiyya ke yi ya kafa tarihi a 2023, sama da dala biliyan $255.8, kari da kashi 0.6 sama da shekarar da ta gabata, in ji shugaba Erdogan.
"Wadannan alkaluma sun haura manufar da muke da ita ta matsakaicin lokaci na samun dala biliyan $255," in ji Erdogan a wurin "Taron Sanar da Alkaluman Fitar da Kayayyaki na 2023" da aka gudanar a ranar Talatar nan.
Bambancin shigowa da fitar da kayayyaki ya karu da kashi 0.8 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata inda a 2023 ya kama kashi 70.7, in ji shugaban kasar, yana mai jaddada cewa gibin kasuwancin kasashen waje na kasar na raguwa duk shekara in ji a 2023 ya kama kashi 3.2.
"In ban da a watan Yuli, gibin kasuwancinmu na shekara ya ragu a watanni bakwai na 2023 da suka wuce," in ji Erdogan. Ya kara da cewa Turkiyya na da manufar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje har na dala biliyan $375, kuma kasar na da karfi da isassun kayan aikin cimma wannan manufa."
A watanni ukun shekarar 2023, Turkiyya ta ci gaba da samun habaka ba kakkautawa da kaso 5.9 a watanni uku sau 13 da suka shude, wanda hakan ya sanya ta zama kasa ta biyu mafi habaka cikin sauri a tsakanin kasashe mambobin G20.
Ci gaba da habaka
Shugaba Erdogan ya bayyana cewa duk da kalubalen da ake fuskanta, Turkiyya na ci gaba da habaka, ci gaba, da kuma samun nasarori masu kyau, ta hanyar dabbaka manufofin habaka da zuba jari, samar da ayyukan yi, samar da kayayyaki da fitar da su ke kawo wa.
Ya karfafa muhimmancin nasarar da aka samu a fannin tattalin arziki, duba da kalubalen da aka fuskanta a 'yan shekarun nan, tun daga ta'addanci da yunkurin juyin mulki da hare-haren da ake kai wa kudadensu.
Da yake karin haske kan tattalin arzikin Turkiyya na habaka da kashi 6 a kowacce shekara a tsakanin 2012 da 2022, habakar da ta haura hasashen duniya na kashi 3.4, Erdogan ya ambaci cewa kalubalen da duniya ta fuskanta irin su Covid-19, matsalar kai komon kayyaki a duniya, rikicin Rasha da Yukren da ma rikicin makamashi da na kayan masarufi ba su iya hana tattalin arzikin Turkiyya habaka ba.
Ya ambaci ci gaban da aka samu wanda zuba jari da kaso 14.7 ya bayar da gudunmowa sosai musamman a watanni ukun 2023, wanda shi ne mafi yawa a 2023. Ya kuma alakanta cewa habakan fitar da kayayyakin kasashen waje ta samu ne sakamakon habakar da aka samu a cikin gida.
Yaki da hauhawar farashin kayayyaki ba saurarawa
Da yake bayyana gamsuwa game da tasirin da samar da kayayyaki ya yi wajen bayar da ayyukan yi, Erdogan ya kuma ambaci cewa an samar da karin ayyuka miliyan hudu a shekaru uku da suka gabata, idan aka kwatanta da kafin barkewar annobar Covid-19.
Erdogan ya jaddada cewa kamar yadda yake a sauran kasashen duniya, babbar damuwar Turkiyya ita ce tashin farashin kayayyaki, wanda tsadar rayuwa ya janyo, ya kuma ce suna ta kokarin sakko da tashin farashin kayayyakin zuwa kasa da kashi 10, ba tare da illata habaka, samar da kayayyaki da ayyukan yi ba.
Ya ce ba za su bayar da dama ga wadanda ba su da godiyar Allah ba su yi amfani da uzururruka wajen yin barazana ga rayuwa, walwala, kadarori da kudaden jama'ar Turkiyya ba.
Game da hanyar da za a bi wajen yaki da tsadar rayuwa, tare da daukar matakn sanya idanu a bangare daya, da kuma dabbaka aiki da dokoki a dayan bangaren, yana mai yakinin cewa kokarin mayar da hankali kan zuba jari, samar da ayyukan yi, samar da kayayyaki, bayar da fifiko ga samar da kudade ga masu fitar da kayayyaki, za su magance hauhawar kayayyakin masarufi a rayuwar 'yan kasa.
A shekarar 2023 mai wahala, wadda ta fuskanci kalubale da jarrabawa da yawa, Erdogan ya bayyana gwagwarmayar da yankin ya fuskanta sakamakon girgizar kasar 6 ga Fabrairu, wadda ta janyo karin nauyin dala biliyan $104 a kan tattalin arzikin Turkiyya.
Duk da asarar rayuka sama da 50,000 da rushewar gine-gine da dama a larduna 11, Erdogan ya yaba wa nasarar Turkiyya wajen sake gyara wadannan yankunan, musamman wajen samar da kayayyakin more rayuwa, bayan "Ibtila'in karni," wanda ibtila'i ne da babu kasar da cikin sauri za ta iya nasarar farfadowa nan da nan sakamakon illar da lamarin ya janyo.
Ya ambaci illar girgizar kasar kan fitar da kayayyaki, wanda ya kai dala biliyan asarar dala biliyan $6.
Yaki da mummunar siyasa
Da yake bayani game da nuna kyama ga Musulunci da kyamatar Larabawa da 'yan adawa suke kara tunzurawa a Turkiyya, Erdogan ya soki yaduwar yadda suka yada tsana da kyama ta hanyar rarraba kawunan jama'a, inda hakan zai illata yawon bude ido a lokacin bazara, wanda daya daga cikin hanyoyin da ke kawo wa kasar kudaden shiga ne.
Ana kuma yunkurin sake kirkirar irin wannan yanayi, a wannan lokacin an yi amfani da harkokin wasanni, tare da goyon bayan jam'iyyun adawa in ji Erdogan. Ya jaddada cewa mutane na fuskantar wulakanci da cin zarafi, har ma da zagi saboda asalinsu "Abu ne da ba za a amince da shi ba".
"Muna fuskantar yanayi mara kyau na nuna kyama da Musulunci da wadanda ba 'yan kasa ba. Abin takaici, 'yan adawa na taka rawa wajen wannan ta'asa, wadda siyasa ce da ke da matukar hatsari da take kawo tsana da nuna kyama."
Da yake ambato kokarin Turkiyya na kara yawan abokan huldarta, Erdogan ya bayyana yadda ake kokarin hargitsa kasar ta hanyar tunzurawa da bayanai marasa kyau na bata suna, musamman wadanda ake yi wuraren da ke da alaka da tarihi, addini, tattakin arziki da kasuwanci.
"Muna sane da yunkurin da ake yi na raba kasarmu daga yankinta na asali, raba ta da kawayenta na yankinta, da kasashe 'yan uwa da suke da babbar alaka ta tarihi, addini, mutuntaka, tattalin arziki da kasuwanci, ta hanyar kalaman tunzura da bata suna."
Ya ce "Tabbas Turkiyya za ta kawo karshen wadannan wasannin, kamar yadda ta yayyaga sauran munanan wasanni na baya."
Shugaba Erdogan ya bukaci masu fitar da kayayyaki da su taka rawa wajen yaki da siyasar nuna tsana da wasu maras akishin Turkiyya da jama'ar kasar. Ya yi kira gare su da su bayar da gudunmowa wajen samar da bayanai ga jama'a, musamman ma matasa.
Yayin da yake nuna gamsuwarsa da masu fitar da kayayyakin da masu assasa kasuwancin da ke aiki don habaka ciniki da samar da kaya kirar Turkiyya a fadin duniya, Erdogan ya yi nuni da yankin da Turkiyya ke ciki mai alfanu da kalubale.
Ya jaddada muhimmancin yankin da Turkiyya take a lamuran duniya, sannan ya bayyana cewa kasar ta yi nasarar kauce wa zamantowa wani bangare na kazamin rikicin da ake a arewaci da kudancin kasar, duk da yunkurin jagororin mayaka da ke son sanya kasar cikin rikicin.
Duk da tsoma bakin wasu daga waje, Erdogan ya karfafa cewa yunkurin nasu na inganta alaka da makota bisa tsarin "nasara ga kowa" da warware takaddama da wasu kasashen yankin yayin da ake habaka hadin kai.
Shugaban ya kuma bayyana kokarin da suke yi wajen daga martabar alakarsu da kasashen duniyar Turkawa masu tarihi, habaka kyakkayawar alaka da Turai da Amurka, da inganta alakarsu da kasashen Afirka da Latin Amurka.