Turkiyya na buƙatar haɓaka alaƙarta da ƙawancen BRICS, kuma za ta halarci taron ranar Laraba sakamakon gayyatar da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi wa ƙasar, in ji Shugaba Recep Tayyip Erdogan.
Jawabin Erdogan na ranar Talata na zuwa ne a lokacin da Rasha ta shirya karɓar baƙuncin taron shugabannin ƙasashe mambobin ƙawancen BRICS a birnin Tatarstan na Kazan.
"Ƙawancen ƙasashen BRICS, wani ɓangare ne mai muhimmanci na G20 kamar Turkiyya, suna da kusan kashi 30 na faɗin ƙasa na duniya da kuma kashi 45 na yawan jama'ar duniyar," in ji Erdogan.
Ya yi tsokaci da cewa ƙasashen BRICS ne ke da kashi 45 na yawan jama'ar duniya, kuma suna samar da kashi 40 na albarkatun mai a duniya inda suke fitar da kashi 25 na kayayyaki a duniya.
"A matsayinmu na Turkiyya, muna son ƙarfafa alaƙarmu da BRICS," in ji Erdogan.
Turkiyya a taron BRICS
Da fari a ranar Litinin, mai bayar da shawara ga Shugaba Putin, Anton Kobyakov ya gana da jakadan Turkiyya a Moscow Tanju Bilgic kuma dukkan ɓangarorin biyu sun tattauna kan yadda wakilan Turkiyya za su halarci taron na BRICS.
"Tawagar Turkiyya za ta halarci taron BRICS a babban matsayi, kuma babbar shaida ce ta sha'awarmu ta shiga ƙawancen. Ba ni da tantama cewa wannan haɗin kai zai samar da ƙarin damarmaki na faɗaɗa alaƙa," in ji Bilgic.
Dukkan ɓangarorin biyu sun tattauna kan haɗin kan tattalin arziki tsakanin Ankara da Moscow, tare da auna buƙatar haɓaka damarmakin zuba jari.
"Ƙasashenmu a hankali suna ƙarfafa alaƙarsu a muhimman ɓangarori. Na yi amanna cewa halartar taron BRICS da Turkiyya za ta yi zai zama babban al'amari da zai bayar da damar samun sabbin ɓangarorin hadin kai da kuma ƙarfafa dangantaka," in ji Kobyakov.
Taron na kwanaki biyu na BRICS ya ƙunshi ƙasashe mambobin ƙawancen na Brazil, Rasha, India, China da Afirka ta Kudu - waɗanda su ne suka fara kafa ƙawancen - daga baya kuma aka shigar da Masar, Ethiopia, Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ciki.