Shugaba Tebboune yana wata ziyarar aiki ne a China tun farkon wannan makon, inda ya gana da Shugaba Xi Jinping na China a ranar Talata. Hoto: Reuters

China za ta zuba jarin dala biliyan 36 a Aljeriya a fannonin da suka hada da masana'antu da sabuwar fasaha da tattalin arziki da sufuri da kuma noma, kamar yadda shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya fada a ranar Talata.

"Ayyukan da yarjejeniyoyin da aka cimma da Chinan manya ne da dukkan kasashen za su amfana da su," in ji Tebboune, a lokacin da yake magana a wajen wani taro a gundumar Shenzhen da wakilan al'ummomin Aljeriya da ke zaune a China.

Shugaba Tebboune yana wata ziyarar aiki ne a China tun farkon wannan makon, inda ya gana da Shugaba Xi Jinping na China a ranar Talata.

Shugaban Kasar Aljeriya a ranar Alhamis ya ce kasarsa na son dangantakar tattalin arziki tsakanin kasarsa da China ta kai matsayi irin na "kyakkyawan tarihin dangantakar siyasa" da ke tsakaninsu tare da bude kofofin zuba jari tsakanin kasashen biyu.

Reuters