A kwanakin baya Tunisia ta yi fatali da sharudan da IMF ta gindaya mata na samun bashi, wanda hakan ya sa ta nemi taimakon Saudiyya. Hoto/Reters

Babban Bankin Tunisia BCT ya ce kasar ta kokarta ta biya kusan kaso 74 cikin 100 na bashin da ake bin ta a kasashen waje.

Zuwa 10 ga watan Satumbar 2023, kasar wadda ke arewacin Afirka ta biya bashin kasashen waje da ya kai dinar biliyan 6.65, kimanin dala biliyan 2.11 kenan, kamar yadda BCT ya sanar.

Kasar ta yi hasashen cewa zuwa karshen wannan shekara, za ta iya biyan basukan da suka kai jimlar dinar biliyan 8.95 wato kimanin dala biliyan 2.83.

Babban bankin kasar ya bayyana cewa kudaden shiga da kasar ta samu ta hanyar masu zuwa yawon bude ido da kuma kudin da ake turawa kasar daga kasashen waje sun taka muhimmiyar rawa wurin biyan wannan bashin.

Rage ciwo bashi

A halin yanzu Tunisia na da kudaden ajiya a asusun waje da suka kai dala biliyan 8.38.

Sakamakon ci gaban da kasar ta samu wurin biyan bashi, yadda Tunisia ke karbo kudi daga kasuwannin kasashen waje ya ragu daga biliyan dala biliyan 1.08 a watan Yuni zuwa dala miliyan 296 a watan Maris din 2023.

Ma’aikatar kudi ta Tunisia ta bayyana cewa kudaden shiga da kasar ke samu daga haraji ya karu da kaso 8.3 cikin 100 inda kuma kudin da ake kashewa a kasafin kudin kasar ya karu da kashi bakwai.

Hakan ya sa aka samu rarar kudi ta dinar miliyan 58.8 wato kimanin dala miliyan 18.7 zuwa karshen Yunin 2023.

A kwanakin baya ne Tunisia ta tafi wurin Saudiyya neman taimako bayan Shugaba Kais Saied ya yi fatali da sharudan Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya IMF kan batun bashi.

A watan Yuli, kasar ta Tunisia da ke Arewacin Afirka ta samu bashin dala miliyan 400 daga Saudiyya inda kuma ta samu kyautar dala miliyan 100 daga kasar bayan ta yi fatali da tayin da IMF ta yi mata wanda Shugaba Saied ya ce na rashin imani ne.

IMF ta bukaci Tunisa kan cewa ta cire tallafin da take bayarwa kan kayayyakin amfanin yau da kullum da kuma kawo sauyi a ofisoshin gwamnati.

Sai dai Mista Saied ya bai kamata masu bayar da basussuka na kasashen waje su rinka kokarin fadin yadda kasashe masu karfin iko za su gudanar da kasashensu ba.

TRT Afrika