Hauhawar farashin da ake biya na koko (cocoa) ya haɓaka kudin shiga da manoman Kamaru suka samu / Photo: Reuters

Hauhawar farashin da ake biya na koko (cocoa) ya haɓaka kudin shiga da manoman Kamaru suka samu, yayin da manyan kasashe masu noma cocoa a duniya wato Ivory Coast da Ghana ke fama da karancin cocao din a kakar bana.

Manoman da dama sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa suna sayar da cocoa a farashin da ya kai daga CFA 2,000 zuwa 2,200 (kwatankwacin dala 3.67) a kowane kilogiram, daga farashin kakar bara na CFA 750 zuwa 1,290.

Makomar cocoa a birnin New York ya yi tashin gwauron zabin da ba a gani ba a shekaru 46 a ranar Litinin yayin da matsalolin amfanin gona a Yammacin Afirka ke kara tsananta kayan abinci a duniya.

Kayan da ake shigarwa a tashar cocoa ta Ghana sun ragu kusan kashi 50 cikin 100 duk shekara a bana, yayin da na Ivory Coast ya ragu da sama da kashi 35%.

Kamaru ba ta sa ran samun raguwar samar da kayayyaki makamancin haka. Tana sa ran kaiwa kusan metrik ton 300,000 na cocoa a shekara, lamarin da ke mai da ita ƙasa ta huɗu mafi samar da cocoa a duniya a cikin 'yan shekarun nan.

“Na samu kudi da yawa daga sayar da cocoa, wanda hakan ya ba ni damar karbar lamuni,” in ji Susan Itoe, wata manomiyar cocoa a kusa da Konye a yankin Kudu maso Yammacin Kamaru.

An saita tabbacin farashin cocoa na kakar shekarar 2023/24 na Kamaru a kan CFA 1,500 CFA duk kilo daya. Amma ainihin farashin da ake biya ga manoma ya ta’allaka ne da kasuwar, kuma ya tashi har ma fiye da haka.

Reuters