Wannan lamari ya jefa ‘yan kasar da dama a cikin rudani, saboda yadda kusan farashin komai a Nijeriya ya dogara ne a kan farashin musayar dala. Hoto: OTHERS

A karon farko darajar naira ta yi irin faduwar da ba a taba gani ba a Nijeriya idan aka kwatanta da dala, inda aka wayi gari a ranar Laraba ana sayar da dala daya a kan naira 1,300 a kasuwar bayan fage a kasar.

Wannan lamari ya jefa ‘yan kasar da dama a cikin rudani, saboda yadda kusan farashin komai a Nijeriya ya dogara ne a kan farashin musayar dala.

Sai dai duk da cewa ba kowane fanni tashin dalar ke shafa ba, musamman kananan kasuwanci amma a wasu lokutan a kan ji masu kananan sana’o’I irin mai yalo da mai rake ma sukan yi korafin cewa tashin dalar ya jawo sun kara farashin kayayyakinsu.

Tashin dalar ya jawo tashin farashin kayan abinci da sauran na amfanin yau da kullum.

Hatta da zinare da mata ke ado da shi, giram dinsa daya ya kai naira dubu tamanin a wannan makon, saboda cewa da dala ake saro shi daga kasashen da ake yin sa.

Mene ne ya haddasa wannan matsala?

Masana tattalin arziki irin su Shuaibu Idris Mikati sun ce babban dalilin da ya jawo wannan matsalar shi ne yadda Nijeriya take shigo da kusan komai daga kasashen ketare.

Sannan akwai masu bukatar dala don biyan kudin makaranta da zuwa asibiti a a kasashen waje da sauransu.

Ya ce “ka ga kenan kullum kasar tana neman dalolin da za ta yi amfani da su wajen sauke wadannan nauyin.”

A cewarsa hakan ke jawo karancinta, a daya bangaren kuma akwai tsananin bukatarta.

“Ga duk abin da ake tsananin bukatarsa kuma babu wadatarsa, to fa dole farashi zai yi sama,” in ji masanin.

Kazalika masu sharhi sun ce Nijeriya ba ta samun daloli sosai kamar yadda take samu a baya daga sayar da danyen man fetur din da take hakowa, wanda hakan na daga cikin manyan dalilin hauhawar farashinta.

To mece ce mafita?

Masana na ganin za a fita daga wannan kangi ne idan Nijeriya ta zama mai dogaro da kai wajen samar da abubuwan bukata a cikin gida tare da rage shigo da kayyaki daga waje, a maimakon haka ma sai dai ita ta dinga fitar da nata, abin da zai kawo mata dalolin lakadan.

Sai kuma batun inganta fannin lafiya da na ilimi ta yadda mutane za su rage rububin kai ‘ya’yansu karatu kasashen waje da fita neman lafiya, tun da duk sai da dala ake iya hakan.

A karshe masu sharhi sun jaddada muhimmancin gyara matatun man fetur na kasar don ta daina sayo tattaccen mai bayan ta sayar da danyensa, lamarin da ke saka ta kashe makudan daloli.

TRT Afrika