Wanda ake ganin zai yi takara da Biden a zaɓe mai zuwa, Donald Trump yana adawa da harmta TikTok. / Hoto: AFP

Shugaba Joe Biden na Amurka ya sha alwashin sanya hannu kan dokar haramta TikTok idan har majalisar dokokin ƙasar ta amince da wani ƙudurin doka kan hakan.

Yayin da yake hira da manema labarai a hanyarsa ta zuwa wani taron yaƙin neman zaɓe a Pennsylvania, Shugaban ya ce zai rattaba hannu kan dokar haramta TikTok matuƙar majalisar dokokin ƙasar da gabatar masa da ƙudurin.

Biden ya faɗi haka ne ranar Juma'a don nuna goyon bayansa kan yunƙurin hana shafin sadarwar mai farin jini daga aiki a Amurka. Shafin ya yi suna wajen masu wallafa bidiyo a manhajarsa.

Yunƙurin na zuwa ne bayan samun ƙaruwar koke daga jami'an gwamnatin Amurka kan dakatar da bayanan Amurkawa daga yiwuwar faɗawa hannun gwamnatin China.

Ƙudurin dokar da ke gaban majalisar dokokin Amurka, ya tsallake matakin Kwamitin Makamashi da Kasuwanci ba tare da wata adawa ba a ranar Alhamis.

Cikin ƙudurin, an nemi kamfanin ByteDance da ke China da ya cire hannun-jarin mallakar kamfanin na TikTok, ko kuma ya fuskanci haramci.

Kakakin majalisar Wakilan Amurka Mike Johnson shi ma ya goyi bayan ƙudurin, kuma ya ce ba jimawa za a gabatar da shi gaban majalisar don kaɗa ƙuri'a.

“Idan suka amince da ƙudurin, zan rattaba masa hannu,” in ji Biden lokacin da 'yan jarida suka masa tambaya kan dokar.

Fadar gwamnatin Amurka ta samar da tallafi a hukumance wajen tsara daftarin ƙudurin, duk da dai sakatariyar yaɗa labarai ta White House, Karine Jean-Pierre ta faɗa a farkon makon nan cewa, har yanzu ƙudurin doka kan TikTok na "buƙatar ƙarin gyara” kafin ya kai matakin da Biden zai amince da shi.

Shi kuwa tsohon shugaban ƙasa, kuma wanda yake dab da zama ɗan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump ya fito a shafin sadarwa na Truth Social ranar Alhamis, ya wallafa cewa yana adawa da haramta TikTok saboda hakan zai ɗaukaka shafin Facebook a fagen gasar kasuwanci.

Trump na nuna wannan adawa ce bayan da a ƙarshe-ƙarshen mulkinsa ya taɓa gabatar da umarnin doka da zai haramnata TikTok da ma shafin WeChat na China, kafin daga baya ya janye umarnin.

Adawa daga Trump ta sa shi karo da wasu jigajigan jam'iyyar Republican a batun muhawara kan TikTok, waɗanda suka haɗa da Kakakin majalisa Johnson, da jagoran 'yan Republican a majalisar Wakilai Steve Scalise, wanda ya kira dokar da “ƙuduri mai matuƙar muhimmanci ga tsaron ƙasa.”

Cibiyar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, da Ma'aikatar Sadarwar ƙasar sun yi gargaɗin cewa kamfanin da ya mallaki TikTok, wato ByteDance zai iya bai wa gwamnatin China bayanan masu amfani da shafin, kamar na inda mutum ya shiga a shafin, da na wuri, da kuma na fayyace mutum.

TikTok dai ya ce bai taɓa yin hakan ba, kuma ba zai yi hakan ba ko da an nemi ya yi. Kuma gwamnatin Amurka ba ta kawo hujjar cewa hakan ya taɓa faruwa ba.

A 2022, Shugaba Biden ya haramta wa ma'aikatan gwamnatin tarayyar ƙasar da suka kai miliyan huɗu amfani da TikTok, kan duk na'urorin da cibiyoyin gwamnati suka mallaka, idan ban da jami'an doka, da kuma masu bincike na tsaron ƙasa.

Duk da dai a baya gwamnatin ta kawo batun tsaron kasa, amma batun yaƙin neman zaɓen Biden shi ma ya hura wutar wannan batu a yanzu.

Idan har ƙudurin ya zama doka, za a haramta TikTok da duk wasu manhajojin kamfanin ByteDance, daga samuwa a shagunan manhaja na Apple ko Google ko kan duk shafin yanar gizo da ke taskace a Amurka.

Sai dai kuma, kamfanin na TikTok ya yi alƙawarin katange bayanan masu amfani da shi da ke Amurka, daga babban kamfanin da ya mallake shi, ta hanyar kafa wani reshen kamfanin da ke da jagoranci mai zaman-kansa, wanda ƙasashen waje za su iya saka wa ido.

Wani rahoton ra'ayin jama'a game da batun haramta TikTok, wanda Associated Press da NORC Center for Public Affairs Research suka gudanar, ya gano cewa Amurkawa sun samu rabuwar kai kan batun manhajar.

Kashi 32 na mutane manya a Amurka sun ce za su goyi bayan haramta amfani da TikTok a faɗin ƙasar. Amma kashi 35 sun ce za su yi adawa da hakan.

Masu amfani da TikTok sun kai miliyan 170 a Amurka, yawancinsu masu ƙarancin shekaru, wanda da wuya su damu idan shafin na yaɗa bayanan masu amfani da shi.

TRT Afrika