Tigran Gambaryan, babban jami'in Binance yana fuskantar shari'a kan guje wa biyan haraji da halatta kuɗin haram a kotun tarayya da ke Abuja, / Hoto: Reuters

Ministan yaɗa labarai na Nijeriya, Mohammed Idris, ya ce ana bin ƙa'ida a shari'ar da ake yi kan kamfanin hada-hadar kuɗi ta intanet na Binance, da kuma ɗaya cikin manyan jami'an kamfanin, Tigran Gambaryan.

A wata sanarwa, ministan ya ce, "An bi ƙa'ida, kuma masu shigar da ƙara suna da tabbaci kan ƙarar, bisa la'akari da bayanai da hujjojin da suka tara. Binance zai samu dukkan damar kare kansa a kotu kan tuhumar laifukan kuɗi da suka yi wa Nijeriya. Ranar 20 ga Yuni, 2024 ne zama na gaba."

Ya kuma bayyana cewa alƙalin da ke shari'ar ya bayyana ƙarara cewa an hana Gambaryan beli ne saboda tsoron zai iya tserewa, ganin yadda abokinsa Nadeem Anjarwalla ya gudu daga ƙasar.

Ministan ya kuma ƙara da cewa, “Changpeng Zhao, biloniya kuma ɗaya cikin wanda suka kafa Binance yanzu yana gidan yari kan hukuncin wata huɗu a Amurka, bayan an same shi da laifin halatta kuɗin haram, bayan da Binance ya amsa laifinsa a fili na tallafawa ta'addanci da almundahana da taimakawa kaucewa kamawa da tallafawa gungun masu yaɗa baɗala da yara ƙanana".

“Hukomomin shari'a sun yi amanna cewa ayyukan Binance a Nijeriya wani ɓangare ne na irin yadda suke aiki a kasashen duniya. Aikin kotunanmu na gida, kamar yadda yake a wasu ƙasashen, shi ne su tabbatar kamfanin ya ɗauki alhakin laifukansa,” cewar Minista Idris.

Binance dai kamfanin hada-hadar kadarori ne a intanet, inda masu amfani da shafin suke cinikayyar kuɗaɗe. A Nijeriya, Binance ya yi hada-hadar sama da dala biliyan $20 a 2023, wanda ya haura kasafin kuɗin fannin lafiya da ilimi, wanda hakan ya ƙarfafa masu dillancin kuɗaɗe da kuma haifar da tsadar rayuwa.

Bugu da ƙari, kamfanin ba shi da rijista a Nijeriya, kuma bai taɓa biyan haraji a ƙasar ba, bayan kuma yana yin aiki ba tare da sa-idon masu kare ayyukan da suka saɓa wa doka ba.

TRT Afrika