Rikicin kungiyar Hamas da Isra'ila ya sanya farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabi / Photo: AA

Farashin ɗanyen mai ya yi tashin gwauron zabi bayan mummunar harin kungiyar Hamas a kan Isra'ila, lamarin da ke zama barazana wajen kara rura wutar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

A safiyar ranar Litinin farashin danyen mai samfurin Brent a duniya ya tashi da kashi 4 cikin dari a tebrin kasuwar kasashen Asiya, inda kowacce gangar mai ta kai dalar Amurka 88.15, sama da dala 84.58 na kasuwar ranar 6 ga Oktoba, lamarin da ya haifar da rashin tabbas ga makomar yankin Gabas ta Tsakiya.

Karin farashin da aka samu ya kara mayar da samfarin Brent kasa duk da cewa a makon da ya gabata farashin ya kai dala 97.69 kan kowacce ganga da aka bayyana a ranar 28 ga watan Satumba.

Duk da cewa yankunan Isra'ila da Falasdinu ba su da wani arzikin samar da mai, amma yankin Gabas ta Tsakiya na samar da kashi uku na man da duniya ke amfani.

Ana ganin matakin karin farashin ya biyo bayan harin karshen makon nan da mayakan Hamas a Gaza suka kaddamar kan kudancin Isra'ila, ba zai yi wani tasiri ba wajen katse samar da mai a duniya.

Akalla ‘yan Isra’ila 700 ne aka kashe tare da sace wasu da dama bayan kawanyar iyakar kasar da mayakan Hamas suka yi a ranar Lahadi, yayin da sama da mazauna Gaza 400 suka mutu a harin mai da martani da Isra’ila ta kaddamar.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a halin yanzu al'ummarsa na cikin yaki, yana mai shan alwashin daukar fansa ''mai karfi.''

A daya bangaren kuma shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya yi kira ga shugaban Hamas ta wayar tarho domin taya shi murnar samun "nasara".

Martanin manyan jagororin biyu daga yankin Gabas ta Tsakiya ya yi nuni kan yadda harin Hamas zai iya dagula dangantaka a tsakanin yankin.

Sai dai wani abin lura a yanzu shi ne, Isra'ila na iya cimma matsaya kan cewa Iran ta taka rawar gani wajen tallafawa ayyukan Hamas, wanda ya haifar da karuwar hare-haren da ake kai wa daular kasashen Musulunci a boye.

Hakan kuma zai rage wa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa kwarin gwiwar daidaita alaƙarsu da Isra'ila a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da rikici da ƙungiyar Hamas, wanda ko shakka babu zai haifar da gagarumar hasarar rayukan Falasɗinawa fararen hula a Gaza.

Rawar da Iran ke takawa a rikicin

Idan har Tehran ta cigaba da bai wa Hamas goyon baya akwai yiwuwar ta janyo wa kanta cikas a kokarinta na kasancewa tare da Saudiyya, kazalika, hakan na iya ƙara yiwuwar gwamnatin Biden ta yi watsi da tsarinta na sassaucin ra'ayi, wanda ya bai wa Iran damar bunkasa fitar da mai a shekarar 2023.

A watan Mayu ne farashin danyen mai da Iran ke fitarwa ya soma ƙaruwa bayan sassaucin takunkumin doka da Amurka ta yi wa kasar, a wani mataki na kokarin gwamnatin Biden na samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Gangar mai miliyan 1.35 da ake fitarwa kullum ya tashi a watan Afrilu zuwa ganga miliyan1.79 a watan Agusta, adadin da zama mafi yawa tun shekarar 2019 bisa bayanan masu nazari kan kayayyakin mai na Kpler.

A takaice da, ana iya cewa nasarar da yakin hamar ya iya cimma shi ne dakatar da yunkurin daidaita dangantakar siyasa a yankin na gabas ta tsakiya.

Tsawaita rikicin da zuwar da jini a Gaza zai mayar da hannun agogo baya a tsarin sannan barazanar rikicin na iya komawa bangaren kasuwaninin mai.

A baya an taba zargin Iran da abokan huldarta wajen ƙaddamar da hare-haren jiragen sama a kan cibiyoyin hakar mai na Saudiyya a watan Satumban 2019, matakin da ya haifar da tashin farshin a kasuwannin duniya.

A yanzu dai babu tabbas kan yadda lamarin zai kasance, amma rashin tabbas da kuma hadarin da ke tattare da abin da ke faruwa su ke janyo fargaba kan sakamakon farashin ɗanyen man.

TRT Afrika