Rana ce ta fadi a bayan wani wurin aikin rijiyar mai ta kamfanin Goldsmith a Texas / Laraba, 9 ga watan Maris, 2022 / Hoto: AP  

Farashin man fetur ya karu da dala 1 a ranar Juma'a, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa sojojin Amurka sun kai hari kan Iraniyawa a Siriya lamarin da ya haifar da fargaba game da dagulewar rikicin Isra'ila da Hamas yanayin da ka iya tasiri ga samar da danyen fetur a Gabas ta Tsakiya.

Farashin danyen samfurin Brent ya karu da dala $1.16, kwatankwacin kashi 1.3 kenan, zuwa dala 89.09 a kan kowace gangar mai da misalin karfe 03:38 agogon GMT.

Kazalika farashin danyen mai samfurin West texas na Amurka WTI shi ma ya haura da dala 1.08 kwatankwacin kashi 1.3, zuwa dala 84.29 kan kowace ganga.

Hare-hare biyu da Amurka ta kai a wasu wurare da dakarun kare addinin Musulunci da kungiyoyin da ke mara musu baya suke zama a Gabashin Siriya, martani ne ga harin da suka kai wa sojojinta da ke Iraki da Siriya, a cewar sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta fitar a ranar Alhamis.

Wadannan hare-haren sun karu tun da aka fara rikicin Isra'ila da Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba. Duk da cewa yanayin da ake ciki bai yi wani tasiri kan samar da fetur ba, amma akwai fargabar cewa rikicin tsakanin Gaza da Isra'ila da Amurka ke mara wa baya da kuma ita kanta Hamas na iya yaduwa tare da kawo cikas ga samar da danyen fetur daga Iran, babbar mai samar da danyen mai wacce kuma ke goyon bayan Hamas.

Kazalika idan yakin da dada girma zai iya yin tasiri ga jigilar fetur daga Saudiyya, daya daga cikin manyan kasashe masu fitar da mai a duniya, da kuma sauran masu samar da danyen mai daga yankin Tekun Fasha.

Brent da WTI suna shirin fitar da bayanan farko kan faduwar farashin fetur na makonni uku.

"A matsayina na dan kasuwa, zan ce mun dan kauce daga matsayinmu a nan- wajen kokarin mai da hankali a rikicin da ya shafi tsarin siyasa wanda bai kawo mana wani cikas ba ga wadatar mai a wajen yankunan Gabashin Bahar Rum na Yammacin Asiya," in ji Kelvin Yew, wani babban dillalin mai a kamfanin saka hannayen-jari na Ocean Leonid.

Tashin 20 cikin 100

Sojojin Isra'ila sun kai hari mafi girma a Gaza a yakin da ya tashi dare daya wanda kuma suka shafe kwanaki 21 suna yi da Hamas, lamarin da ya harzuka kasashen Larabawa.

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce har yanzu sojojin kasar na shirye-shiryen kai wani babban farmaki ta kasa, yayin da Amurka da sauran kasashe suka bukaci Isra'ila da ta jinkirta, saboda fargabar yaduwar tashin hankali a wasu bangarorin Gabas ta Tsakiya.

"Zai yi matukar wahala a iya hasashen yadda za a wanye a wannan rikicin domin akwai yiwuwar a samu karin kasashe da za su iya shiga cikinsa," a cewar wani mai sharhi a cibiyar kasuwanci ta RBC Capital Helima Croft.

Manazarta daga kamfanin zuba hannayen-jari na Goldman Sachs sun yi hasashen farashin danyen mai na Brent zai kai dala 95 kan kowace ganga a wata hudu na farkon 2024, sai dai sun yi kari da cewa rage fitar da fetur daga Iran zai iya sanya farashin ya tashi.

Farashin zai iya kai wa kashi 20 cikin 100 idan har aka samu katsewar kasuwanci ta mashigin tekun Hormuz inda kashi 17 cikin dari na jigilar mai a duniya ke bi, a cewar sanarwa manazartar.

TRT World