Isra'ila ta sa hannu kan yarjejeniyar sayen jiragen yaƙi na dala biliyan 5.2 daga Amurka

Isra'ila ta sa hannu kan yarjejeniyar sayen jiragen yaƙi na dala biliyan 5.2 daga Amurka

Za a sayi jiragen da tallafin soji da Amurka ke baiwa Isra'ila, in ji Ma'aikatar Tsaro.
Jirgin sama na yaki samfurin F-15 ya tashi sama a lokacin bikin yaye daliban sojin saman Isra'ila a sansanin Hatzerim da ke kiudancin Isra'ila a ranar 29 ga Yuni, 2023. / Photo: Reuters

Isra'ila da ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza da Lebanon, a ranar Alhamis ta sanar da sanya hannu kan yarjejeniyar sayen jiragen yaƙi samfurin F-15 guda 25 daga kamfanin Boeing na Amurka.

A wata sanarwa, Ma'aikatar Tsaro ta Isra'ila ta bayyana cewa ta cim ma yarjejeniya a ranar Laraba, wadda wani bangare ne na tallafin soji da gwamnatin Amurka da Majalisar Dokoki suka amince su ba ta, wanda ya hada da zaɓin ƙarin jiragen yaƙin 25.

Za a inganta jiragen da tsarin harba makamai na zamani, sannan a saka musu fasahar zamani ta Isra'ila, in ji sanarwar.

Ma'aikatar ta kuma ce jiragen yaƙin da aka ƙara ƙarfi da ingancinsu za su taimaka wa dakarun sama "Cigaba da bayar da fifiko wajen magance ƙalubaen yau da na gobe a Gabas ta Tsakiya."

A shekarar 2031 za a fara miƙa jiragen saman, inda duk shekara za a dinga bai wa Isra'ila jirage huɗu.

A hare-haren da Isra'ila ta fara kai wa tun 7 ga Oktoban 2023 a Gaza, an kashe Falasɗinawa sama da 43,000, mafi yawan su mata da yara ƙanana.

Rikicin ya kuma yaɗu a Lebanon, inda hare-hare ta sama da ta kasa na Isra'ila suka kashe sama da mutane 3,000 tun bayan afka wa Gaza.

TRT World