Wata sanarawa daga kakakin babban kamfanin mai na Nijeriya, NNPCL ya fitar a yammacin Alhamis ta ce, kamfanin ya shawo kan 'matsalar jigilar mai' da ta haifar da ƙarancin mai a sassan ƙasar.
A cewar sanarwar, matsalolin da suka shafi jigilar man zuwa sassan ƙasar su ne ummul aba'isin ƙarancin man da aka yi fama da shi a baya-bayan nan, wanda rahotanni suka nuna cewa ya haifar da ƙaruwar farashin man a wasu jihohin Nijeriya.
Sakamakon ƙarancin man, an yi ta ganin jerin gwanon motoci a gidajen sayar da mai, waɗanda suke ɗaukar lokaci kafin su sha man.
Kakakin kamfanin, Olufemi Soney ya faɗa a sanarwar cewa "Kamfanin NNPCL yana fayyace cewa matsin da ake samu kan wadatuwar man fetur na PMS a wasu wurare a ƙasar, ya samo asali daga matsalar jigila wadda aka shawo kanta".
Sanarwar da babban jami'in hulɗa da jama'a na kamfanin ya sanya wa hannu, ta ƙara da cewa kamfanin “yana jaddada cewa farashin albarkatun mai bai sauya ba.”
Sakamakon haka ne kamfanin na NNPCL ya yi kira da 'yan Nijeriya da su gujewa “rige-rigen sayan man tun da akwai isasshen albarkatun mai a ƙasar”.