Motar sojojin Isra'ila ta bangara zuwa iyakar Gaza, kamar yadda aka hango daga kudancin Isra'ila. / Hoto: Reuters

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza zai iya lashe ƙarin dala biliyan 14 a shekarar 2024, adadin da ya ninka gibin kasafin kudinta kusan sau uku, in ji Ma'aikatar Kudi, inda ta yi hasashen za a ci gaba da yakin har nan da watan Fabrairu.

Da yake bayar da bayanai ga 'yan majalisar dokoki, mataimakin kwamishinan kudi na ma'aikatar, Itai Temkin a ranar Litinin din nan ya ce yaƙin na iya kaiwa har nan da watanni biyu na cikin shekara mai zuwa ta 2024, inda ya kara da cewa an ware dala biliyan 8.3 don tsaro, dala biliyan 5.5 kuma don kula da fararen hula.

Ya shaida wa majalisar ta Knesset cewa hakan zai kara kudaden da aka warewa tsaro da sama da dala biliyan 13.2, wanda ya haura adadin da aka warewa bangaren a baya.

Kasashen kudin shekarar 2024 zai karu zuwa dala biliyan 155.5 daga dala biliyan 142.1 da aka tsara kashewa, wanda hakan ya kaso gibin kaso 5.9. daga gibin 2.25.

Tare da gibin da ake sa ran a shekara mai zuwa zai karu da dala biliyan 20.7 zuwa biliyan 31.5, inda Temkin ya ce za a rage kashe kudade a wasu bangarorin ko kara yawan haraji.

Ya kuma bayyana cewa a yanzu ba a da masaniyar ko yakin na Gaza zai kai har watan Maris ko ya haura shi.

Ya ce "Akwai yiwuwar a ciki shekarar za mu dawo mu sake sabunta kasafin, a yayin da ake ci gaba da yakin."

TRT World