Ghana za ta fuskanci katsewar wutar lantarki na makonni uku, in ji sanarwar. / Hoto: AFP

Kamfanonin wutar lantarki na Ghana GRIDCo da ECG sun sanar da cewa za a fuskanci katsewar wutar lantarki na tsawon makonni uku a wasu sassan ƙasar sakamakon ƙarancin gas daga Nijeriya.

"An fuskanci ƙarancin gas ne sakamakon gyare-gyare da sashen samar da gas na Nijeriya ke yi wanda aka yi hasashen zai ɗauki tsawon makonni uku kafin a kammala," a cewar sanarwar da GRICo da ECG da kuma kamfanin bututun iskar gas na yammacin Afirka WAPCo suka fitar a ranar Alhamis.

''GRIDCo da ECG na son sanar da jama'a cewa sakamakon raguwar gas daga Nijeriya tun daga ranar 12 ga watan Yunin 2024 wasu yankuna a faɗin ƙasar sun samu katsewar wutar lantarki,'' in ji sanarwar.

Aikin gyaran ya haifar da raguwar ƙarfin samar da wutar lantarki a sassa da dama a faɗin Ghana, lamarin da ka iya janyo tsaiko a aikin rarraba wutar lantarki a tsawon lokacin aikin.

Kazalika sanarwar ta ce ''kamfanonin GRIDCo da ECG na son ƙarfafa gwiwar al'ummar Ghana cewa za mu haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki a fannin makamashi don inganta albarkatun da ake da su da kuma rage tasirin da rage yawan gas ɗin zai yi ga masu amfani da shi."

GRIDCo and ECG wish to inform the public that due to a reduction in gas supply from Nigeria since 12th June, 2024 some...

Posted by Ghana News Agency on Thursday, June 13, 2024

Ghana na cikin ƙasashen yammacin Afirka da ke yawan fama da katsewar wutar lantarki, domin ko a makon jiya sai da wasu 'yan ƙasar suka gudanar da zanga-zanga kan yawan ɗauke lantarki.

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya buƙaci gwamnatin Ghana ta inganta tsarin tafiyar da harkokin makamashin ƙasar domin magance matsalar wutar lantarki a ƙasar.

TRT Afrika da abokan hulda