A wani mataki na ƙarfafa danganta tsakanin Nijeriya da Equatorial Guinea, Shugaba Bola Tinubu tare da takwaransa Teodoro Obiang Nguema Mbasogo sun rattaba hannu a yarjejeniyar kafa aikin bututun iskar gas.
Yarjejeniyar, wadda aka kulla a yayin ziyarar aiki ta kwanaki uku da Shugaba Tinubu ya kai kasar Equatorial Guinea, za ta taimaka wajen inganta hanyoyin samar da iskar gas tare da lalubo sabbin ayyukan yi a yankin, in ji sanarwar da babban mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan kafofin yada labarai ya fitar a ranar Alhamis ta shafin X.
Kazalika yarjejeniyar wadda a kan sanya wa hannu a ranar Laraba a babban birnin Malabo ta Equatorial Guinea ta shafi bangarori daban-daban masu mahimmanci, da suka hada da matakan doka da ka'idoji game da kafa bututun iskar gas ɗin tare da hanyoyin tafiyar da aikin gaba ɗaya.
Shugaba Tinubu dai ya jaddada muhimmancin yarjejeniyar, inda ya ce za ta bude sabbin hanyoyin samar da iskar gas da kuma ayyukan yi, tare da taimakawa wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasashen biyu.
Shugabannin ƙasashen biyu sun nuna ƙwarin gwiwarsu bisa ga alfanun da yarjejeniyar za ta haifar a yankin.
Haka kuma shugabannin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi tashe-tashen hankula da kuma hanyoyin magance rikice-rikice a Afirka tare da inganta zaman lafiya
''Mun tattauna batun inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashenmu, tare da hanyoyin samar da ci gaba a nahiyarmu,'' in ji Shugaba Tinubu.
Arzikin iskar gas a Nijeriya
Nijeriya dai ta kasance kasa wadda ke kan gaba ta fuskar arzikin makamashi a nahiyar Afirka.
A wani rahoto da hukumar kula da sa ido da kuma ɓunkasa ƙirkira ta Nijeriya NCDMB ta fitar, ta ce an ƙiyasta cewa Nijeriya na da tan triliyan 209 na cubic feet na iskar gas da ke shimfiɗe a ƙasar.
Wannan ɗimbin albarkatu sun sanya kasar a sahun gaba wajen ƙoƙarin ƙarfafa tsaron makamashi, a fadin Afirka da kuma samar da makamashi mai tsafta ga sauran kasashen duniya.
A shekarar 2016 ne, Nijeriya ta ɗauki wani gagarumin mataki amfani da damar da take da shi wajen hada kai da Moroko don gina bututun iskar gas na Nijeriya- Moroko (NMGP).
An yi ƙiyasta aikin gina bututun na NMGP wanda ya samu goyon bayan ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) zai laƙume dala biliyan 25.
Sannan tsawonsa zai kai kilomita 5,600 tsakanin Nijeriya da Moroko, kana ana sa ran zai samar da murabba'in iskar gas biliyan 30 a duk shekara.
Kazalika an yi hasashen aikin zai biya buƙatun makamashi na mutum miliyan 400 a Afirka ta hanyar haɗa ƙasashe 13 da Tekun Atlantika.