Nijeriya ce kan gaba wajen samar da mai da iskar gas amma tana fama da bukatun karancin makamashin cikin gida. Hoto: Reuters  

Asusun ajiya na zuba hanayen jarin Nijeriya ya kaddamar da wani shirin zuba jari a aikin samar da makamashi mai tsafta (RIPLE) na dala miliyan 500 da nufin inganta hanyoyin samar da wutar lantarki a kasar.

Hukumar Kula da Zuba Jari ta Nijeriya (NSIA) ta ce wannan yunƙuri zai mayar da hankali ne a samar da ci gaba da saka hannayen jari tare da gudanar da shirye-shiryen da suka shafi fannin tsaftataccen makamashi a Nijeriya.

Za a fara gudanar da aikin farko na shirin RIPLE a cibiyar masana’antar Tokarawa da ke jihar Kano a yankin arewacin kasar, a cewar sanarwar hukumar a ranar Litinin.

Nijeriya, wacce take da yawan al'umma fiye da mutum miliyan 200 tana samar da wutar lantarki kusan megawatt 4,000 ne kacal a kowacce rana, adadin da ke kasa da bukatun al'ummar kasar.

Kazalika katsewar wutar lantarki a kasar na yawan haifar da ruɗu a fadin kasar.

Kawar da hayakin carbon

Shirin zai samar da wani tsari tare da rarraba wutar lantarki mai karfin megawatt 70 ga masana’antu da cibiyoyin kasuwanci da sauran al'ummar a yankunan da ke dauke da hanyoyin sadarwar wutar lantarki kusan 9,000, a cewar hukumar NSIA.

Nijeriya na yawan dogara kan iskar gas wajen samar da wutar lantarkinta, a yanzu haka kasar tana da burin bunkasa yawan hanyoyin samar da tsaftataccen wutar lantarki daga kashi 13 cikin 100 a shekarar 2015 zuwa kashi 23 cikin 100 nan da 2025.

Sannan kuma zuwa 36 cikin 100 nan da shekarar 2030 a jimillance, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Hukumomi a kasar sun ce kaddamar da wannan aikin zai biyo bayan yarjejeniyar hadin gwiwa da Hukumar Kudi ta Duniya (IFC), wani bangare na rukunin Bankin Duniya don "ƙara sake fasalin yanayin makamashin Nijeriya," ko da yake ba su yi karin bayani ba kan matakin.

Ko da yake hukumomin NSIA da Vitol sun kaddamar da makamacin irin wannan aiki a wannan Afrilu don saka hannun jari a fannoni daban-daban na kawar da iskar carbon da sauran ayyuka a kasar mafi yawan al'ummar a nahiyar Afirka.

TRT Afrika