An samu gagarumar riba da ba taba ganin irinta ba a hada-hadar kudaɗe ta intanet a Nijeriya, inda ta haura sama da Naira tiriliyan dubu a shekarar 2024, a cewar wani rahoto da hukumar da ke kula da harkokin bankuna a Nijeriya (NIBSS) ta fitar.
Hukumar ta ce sashenta da ke sa ido kan biyan kudaɗe kai-tsaye (NIP) ya bayyana samun ƙarin riba ta kaso 79.6 cikin 100 wato sama da Naira tiriliyan 600 da aka samu a shekarar 2023.
A ɓangare guda kuma bayanan hada-hadar kuɗi kai-tsaye ta intanet ya nuna yadda aka yi ta samun ƙari a cikin dukka watanni 12 na shekarar, inda ribar da samu a watan Disamba ta zarce ta sauran watannin.
Ratohon ya ƙara da cewa 'yan Nijeriya sun kashe jimillar Naira triliyan 115.1 a watan Disamban 2024 ta hanyar hada-hadar kudaɗe ta intanet, ko da yake an yi la'akari da lokacin bukukuwan ƙarshen shekara inda mutane ke yawan kashe kudaɗe.
Alƙaluman NIBSS na shekarar 2024 sun kasance adadi mafi yawa da hukumar ta taɓa samu a bayanan tsarin kudaɗen intanet na wata-wata da take tattarowa.
Haka kuma yawan hada-hadar cinikayya da NIBSS ta tattaro na shekarar ya ƙaru daga Naira biliyan 9.7 a shekarar 2023 zuwa Naira biliyan 11.2 a shekarar 2024.
Adadin kuɗin na wakiltar ƙarin kaso 15.5 cikin 100 na yawan hada-hada ta intanet da aka yi a shekarar.
Ƙwararru dai na alaƙanta wannan ƙarin da aka samu da ƙarancin tsabar kuɗi da 'yan Nijeriya suka yi ta fama da shi a baya bayan nan da kuma tsarin rage amfani da kuɗi kai-tsaye da babban bankin ƙasar (CBN) ya fitar da shi da nufin taƙaita yawan kuɗaɗen da za a iya cirewa daga bankuna a kullum.