NNPCL ya fara gina tashohin iskar gas din LNG a Kogi/ Hoto: Reuters

Kamfanin man fetur din Nijeriya NNPCL, a ranar Alhamis ya ƙaddamar da fara gina tashoshin iskar gas nau’in Liquefied Natural Gas (LNG) guda biyar a garin Ajaokuta na jihar Kogi.

NNPCL ya ce ya ɗauki matakin ne don faɗaɗa hanyoyin samar sarrafa iskar gas a cikin gida kana ana sa ran hakan zai bunƙasa wadatuwar makamashin a cikin ƙasar tare da taimaka wa masana’antu da kuma samar da ayyukan yi.

Yayin bikin ƙaddamar da fara gina tashoshin, Shugaban Kamfanin NNPCL Mele Kyari ya ce an zabi a gina tashoshin ne a jihar Kogi saboda la'akari da yadda ake da manyan bututan kamfanin a wurin da aka yi tashoshin.

Sannan ya ce akwai iskar gas a bututan kamfanin wanda hakan ya sa cikin sauki za a yi amfani da ita wajen aikace-aikacen gina tashoshin da za a yi.

Kazalika shugaban ya ce Shugaba Bola Tinubu ya dukufa wajen sauya alkiblar makamashin kasar zuwa iskar gas a wannan lokaci a Nijeriya saboda yadda kasar take da dimbin arzikin iskar gas.

Mele Kyari ya ce iskar gas za ta iya zama sila ta sauya ababen hawa wadanda za su kawo ci gaba da bunkasar kasa.

TRT Afrika