Fadar White House ta ce manufar harajin ita ce matsa wa Mexico da Canada da China lamba su ƙara ba da haɗin kai kan daƙile shigar da miygaun ƙwayoyi da tsaron kan iyakoki. / Hoto: AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin sanya harajin 25% a kan kayayyakin Kanada da Mexico da kuma 10% kan kayayyaki daga China daga ranar Talata, don magance matsalar shigar da maganin kashe raɗaɗi na fentanyl da matsalar ‘yan gudun hijira da ke shiga Amurka ba bisa ƙa’ida ba, in ji jami’an fadar White House.

Za a sanya wa albarkatun makamashi daga Kanada haraji kaɗan, 10%, in ji Fadar White House a ranar Asabar.

"Shugaba Donald Trump na ɗaukar ƙwararan matakai don kare Amurkawa daga matsalar maganin na fentanyl. Fentanyl shi ne kan gaba wajen sanadin mutuwar Amurkawa masu shekaru 18 zuwa 45," in ji wata sanarwa.

Amurka ta zargi masu safarar miyagun ƙwayoyi na Mexico da kasancewa "kan gaba a duniya wajen safarar" fentanyl da sauran ƙwayoyi, yana zargin akwai ƙawance tsakanin masu safarar da gwamnatin Mexico.

Game da Kanada, Fadar White House ta yi ƙarin haske game da karuwar samar da maganin na kashe raɗaɗi na fentanyl da kuma tsallaka wa da shi kan iyaka ba bisa ƙa’ida ba, tana mai cewa: "An kama fentanyl a kan iyakar arewa a bara wanda zai iya kashe Amurkawa miliyan 9.8."

An soki China saboda zargin tana taka rawa wajen bayar da tallafi ga kamfanonin sinadarai wajen fitar da fentanyl zuwa kasashen waje, inda fadar White House ta yi iƙirarin cewa: "Ba wai kawai China ta gaza wajen daƙile tushen haramtattun kwayoyi ba, har ma tana taimaka wa wannan kasuwanci."

Martanin Canada da Mexico

Kasashen Canada da Mexico sun sanar da daukar matakan ramuwar gayya kan harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya dora wa kayayyakinsu.

A ranar Asabar, Firaministan Canada Justin Trudeau ya ce Canada za ta sanya harajin 25% kan kayayyakin Amurka da suka kai dala biliyan 106.5 a matsayin martani ga harajin Amurka.

Harajin dala biliyan 20 zai fara aiki daga ranar Talata, sannan na dala biliyan 86 zai fara aiki a cikin kwanaki 21, kamar yadda Trudeau ya shaida wa wani taron manema labarai.

Trudeau ya yi gargadin cewa harajin zai cutar da Amurka, wacce daɗaɗɗiyar ƙawar ƙasar ta Canada ce

Ya nemi mutanen Canada su riƙa sayen kayayyakin da aka yi a ƙasar, kuma su riƙa gudanar da hutu a gida maimakon a Amurka.

Ya ce ana kuma duba wasu matakan da ba na haraji ba, da suka hada da wasu da suka shafi ma'adanai masu mahimmanci da sayen makamashi da sauran ɓangarorin haɗin gwiwa.

Trudeau ya kuma kara da cewa, ƙasashen Canada da Mexico suna aiki tare don fuskantar harajin da Washington ta ɗora wa kayayyakinsu.

Fadar White House ta ce manufar harajin ita ce matsa wa Mexico da Canada da China lamba su ƙara ba da haɗin kai kan daƙile shigar da miygaun ƙwayoyi da tsaron kan iyakoki.

TRT World