Farashin man fetur ya fadi a kasuwa a ranar Juma'a bayan tagomashin da ya samu a baya-bayan nan, yayin da Rasha da Saudiyya ke sa ran kara yawan man da za su fitar, yanayin da ya zarce hasashen buƙatar samun mai daga China a lokutan hutu na ƙasar.
An samu ragin cent 21 daga dala 95.17 a kowace gangar mai a hasashen watan Nuwamba kan farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya na Brent da ya zo karshe a ranar Juma'a.
Kazalika an samu ragin Cent 10 a cinikin Brent na watan Disamba kan dala 93 a kowace gangar mai da misalin karfen 12.55 na dare agogon GMT.
Hasashen danyen mai na Amurka West Texas Intermediate (WTI) ya fadi da Cent 8 zuwa dala 91.63 kan kowacce ganga.
Farashin man fetur ya ragu da kusan kashi 1 cikin 100 a ranar Alhamis, yayin da ‘yan kasuwa suka samu riba bayan da farashin ya yi tashin gwauron zabi a tsawon wata 10, wasu kuma na fargabar cewa yawan kudin ruwa na iya rage bukatar man.
"A dare daya farashin man fetur ya dakatar da gangamin baya-baya nan," a cewar wata sanarwa da Bankin Ostiraliya ta fitar.
"Taron kungiyar OPEC na mako mai zuwa (ranar 4 ga watan Oktoba) zai zama wata muhimmiyar hanya ta sabunta kasuwanni da kuma yiwuwar rage yawan man da kamfanin Aramco ke samarwa," in ji sanarwa
A halin yanzu an samu matsi sosai a kasuwar mai, inda Saudiyya da Rasha da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC da kawayenta da kuma wani bangare na kungiyar OPEC+ suka samu ragin ganga miliyan1.3 a kowace rana har zuwa karshen shekara.
A 'yan kwanakin nan ne Rasha ta sassauta dokar hana fitar da mai wacce ta bullo da ita don daidaita kasuwannin cikin gida, matakin da manazarta ke ganin ba zai wani dade ba saboda yiwuwar hakan ka iya shafar ayyukan matatun mai da kuma tasirin dangantakar cinikayya.
Kasar Turkiyya da Brazil da Maroko da Tunisiya da kuma Saudiyya na daga cikin manyan kasashen da Rasha za ta kai man diesel dinta a wannan shekara, a cewar JPMorgan.
"Tsawaita haramcin fitar da kayayyaki mai zai yi mummunan tasiri ga dangantakar kasuwanci tasakanin sabbin abokan cinikaiya da kamfanonin mai na Rasha suka kulla cikin shekara daya da rabi," a cewar JPMorgan.
Makon Hutu
Rasha ba ta yi wata tattaunawa kan yiwuwar kara samar da danyen mai ba don rama haramcin fitar da man da Moscow ta yi da kungiyar OPEC+, in ji Kremlin.
Bayanan tattalin arziki na baya-bayan nan tare da hutun mako a China wanda aka fara a ranar Juma'a sun taimaka wajen kara yawan bukatun mai a duniya.
Tattalin Arzikin Amurka na kan gabar ci gaba a zangon na biyu kuma alamu sun nuni kan cewa ayyukan kasar ya habaka a cikin wannan zango, a cewar wasu bayanai da aka fitar a ranar Alhamis.