An tallafa wa matakin da dala biliyan 40 daga Bankin Ci-gaban Afirka da Bankin Duniya. Hoto: Tinubu/X

Shugabannin Afirka sun ƙudiri aniyar samar da lantarki mai rahusa ga mutane miliyan 300 a faɗin nahiyar a cikin shekaru biyar.

An sanar da alkawarin da aka kira da 'Yarjejeniyar Makamashi ta Der es Salaam' a lokacin Babban Taron Makamashi na Afirka a ranar Talata a Babbar Cibiyar Taro ta Julius Nyerere ta Ƙasa da Ƙasa da ke gabashin Tanzaniya.

Taron da shugabannin kasashen Afirka 25 da wakilai 1,000 suka halarta, ya mayar da hankali kan "Aiki ga 300", da ke ƙarin haske kan bukatar gaggawa ta warware gibin makamashi a Afirka. A yanzu haka, mutane miliyan 71 ba sa samun lantarki, wanda ke kawo babban nakasu ga habakar tattalin arziki.

"Wannan yarjejeniya na bayyana wata gaɓa mai muhimmanci ga makomar makamashi a Afirka," in ji Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan. "Mun kudiri aniyar samar da makamashi mai rahusa, tsayayyiyar lantarki don sauya rayuwa da tattalin arziki a fadin nahiyar."

Inganta kayan more rayuwa

Shugabannin sun jaddada ƙudirinsu na zuba jari a samar da makamashi mai tsafta, ciki har da hasken rana da na ruwa, da yin alkawarin inganta kayan more rayuwa, tare da aiwatar da tsare-tsaren da za su ja hankulan masu zuba jari.

Tanzaniya, babbar mai taka rawa a Ayyukan Samar da Makamashi a Gabashin Afirka, na shirin kara yawan lantarkin da take samarwa da karin megawatt 2,463 nan da shekarar 2030, ina ake bukatar dala biliyan 13.

An tallafa wa matakin da dala biliyan 40 daga Bankin Ci-gaban Afirka da Bankin Duniya, in ji shugaban Bankin Ci-gaban Afirka Dr. Akinwumi Adesina, yana mai jaddada cewar cim-ma manufar makamashi ta bai-ɗaya na da muhimmanci ga ci-gaban tattalin arzikin Afirka.

Yarjejeniyar ta Dar es Salaam ta kunshi dabaru na rage kudaden wutar lantarki, da rage dogaro kan itatuwa, da habaka samar da makamashi mai tsafta, tana mai sanya kyakkyawan fata da makomai mai inganci kuma mai dorewa ga miliyoyin 'yan Afirka da ke nahiyar.

TRT Afrika