A watan jiya, gwamnatin jihar Ribas ta bai wa rundunar sojin sama ta ƙasar kyautar jiragen ruwa shida domin ƙarfafa yaƙi da ɓarayin danyen man fetur a yankin.

Gwamnatin Nijeriya ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ɓarayin man fetur a yankin Neja Delta a yayin da take shirin fitar da gangar mai miliyan 3 a kowace rana a shekarar 2025.

Nijeriya wadda ke cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen fitar da ɗanyen fetur a Afirka tana samun yawancin kuɗin shigarta daga mai, kuma tana samun fiye da kashi 90 na kuɗaɗen ƙasashen waje daga sayar da man fetur, amma tana fama da ɓarayin mai.

A yayin da gwamnatin ƙasar ta yi ƙiyasin fitar da ganga miliyan 2.06 ta man fetur a kasafin kuɗinta na shekara mai zuwa, a zahiri fetur ɗin da take fitarwa bai wuce ganga miliyan 1.8 a kowace rana ba, a cewar alƙaluman da hukumomi suka fitar.

Ma'aikatar man fetur da rundunar sojin sama ta Nijeriya sun ƙaddamar da yaƙi da ɓarayin danyen fetur, mai suna Delta Sanity (OPDS), a shekarar da ta wuce.

Babban Hafsan sojin sama na ƙasar Emmanuel Ogalla ya ce yanzu wannan shiri na OPDS ya shiga zango na biyu, inda za su yi amfani da jirage marasa matuƙa da helikwafta da ƙarin jami'an leƙen asiri wajen ganin sun rage matsalar, inda suke sa rai za a riƙa fitar da ɗanyen mai da ya kai ganga miliyan uku a kowace rana.

"Idan ka dubi yadda lamura suke a bara, lokacin da muka ƙaddamar da wannan shiri, muna samun gangar ɗanyen fetur miliyan 1.4 kowace rana. Yanzu ya ƙaru zuwa ganga miliyan 1.8.

"Na yi amanna cewa idan muka kammala ɗaukar wadannan matakai, za mu cim ma manufarmu ko ma mu haura ƙiyasin da muka yi," a cewar Ogalla a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata bayan ya ƙaddamar da sabon shirin yaƙi da ɓarayin ɗanyen man fetur a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas.

Ƙaramin Ministan Harkokin Man Fetur Heineken Lokpobiri ya ce adadin ɗanyen fetur ɗin da Nijeriya take fitarwa da kaɗan ya wuce ganga miliyan 1 a kowace rana lokacin da ya soma aiki a watan Agustan 2023.

"Burinmu shi ne mu riƙa fitar da ganga miliyan 3 a kowace rana daga yanzu zuwa shekarar 2025 kuma muna da ƙwarin gwiwa cewa ƙaddamar da yaƙi da ɓarayin mai da muka yi a zango na biyu, wato OPDS zai taka muhimmiyar rawa wajen cim ma wannan manufa."

A watan jiya, gwamnatin jihar Ribas ta bai wa rundunar sojin sama ta ƙasar kyautar jiragen ruwa shida domin ƙarfafa yaƙi da ɓarayin danyen man fetur a yankin.

Reuters