Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bai wa 'yan kasuwa izinin sayen man fetur kai tsaye daga Matatar Dangote.

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bai wa 'yan kasuwa izinin sayen man fetur kai tsaye daga Matatar Dangote ba tare da bi ta hannun kamfanin mai na ƙasar NNPCL ba.

A wata sanarwa da Ma'aikatar Kudi da Tattalin Arziki ta Nijeriya ta fitar a ranar Juma'a, mai ɗauke da sa hannun Ministanta Wale Edun, ya ce wannan mataki ya biyo bayan umarnin da aka bayar ne a Taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, da kuma ƙaddamar da sabon matakin yin cinikin da naira kawai.

"Sabon Tsarin Ciniki Kai Tsaye: Muhimmin sauyi a ƙarƙashin wannan sabon mulki shi ne 'yan kasuwar man fetur a yanzu za su iya sayen fetur kai tsaye daga matatun mai na cikin gida," in ji ministan, wanda shi ke jagorantar kwamitin sayar da danyen da tataccen mai da kudin naira.

Ya ƙara da cewa "Wannan mataki ya nuna yin bankwana da tsohon tsarin da kamfanin NNPCL yake zama ta hannunsan kawai za a sayi man fetur daga matatu."

A yanzu wannan matakin zai bai wa 'yan kasuwar za su iya ciniki kai tsaye da matatun man, lamarin da ministan ya ce zai taimaka wajen sauƙaƙa kasuwancin.

Mista Edun ya ce a taron kwamitin na ranar 10 ga watan Oktoba, an kuma amince cewa fara sayar da fetur din ga 'yan kasuwa zai kawo sauyi mai kyau ga masana'antar.

TRT Afrika