A ranar Alhamis ne aka fara gudanar da taron na AGOA a ƙasar Afirka ta Kudu, inda kasashen Afirka 40 ke halarta. Hoto: Reuters

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya ce gwamnatin Shugaba Joe Biden tana so ta yi aiki da Majalisar Dokoki don inganta shirin kasuwanci na Amurka-Afirka (AGOA).

Mista Blinken ya bayyana hakan ne a wani saƙon bidiyo da ya yi wa taron kasuwanci na Amurka da Afirka da ake gudanarwa a ƙasar Afirka ta Kudu a ranar Juma’a.

Wakiliyar Kasuwanci ta Amurka Katherine Tai ta shaida wa taron cewa Amurka ta yi amannar akwai dama ta inganta shirin kasuwancin Amurka da Afirka don ƙarfafa shi sosai.

A shekarar 2000 ne aka amince da shirin na Yarjejeniyar Habaka Tattalin Arziki da Samar da Damarmaki na African Growth and Opportunity Act (AGOA), a lokacin mulkin Shugaba Bill Clinton, don ƙarfafa alaƙar kasuwanci da yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka.

Kazalika shirin yana da muradin taimakon ƙasashen Afirka su haɓaka tattalin arzikinsu, da samar da yanayin kasuwanci marar haraji a kasuwar Amurka.

Ƙasashen Afirka suna ƙoƙarin ganin an ƙara wa’adin shirin da shekara 10 ba tare da sauye-sauye ba, saboda bai wa harkokin kasuwanci da masu zuba jari da suke da damuwa a kan makomar AGOA, tabbaci.

Taron Afirka ta Kudu

A ranar Alhamis ne aka fara gudanar da taron na AGOA a ƙasar Afirka ta Kudu, a daidai lokacin da Pretoria da Washington ke ƙoƙarin gyara dangantakarsu.

Amurka na ganin Afirka ta Kudu na ƙara kusantar Rasha – wacce babbar abokiyar adawar Ƙasashen Yamma ce.

Ministoci daga kusan ƙasashen Afirka 40 da suke cikin shirin yarjejeniyar AGOA ne suke halartar taron a birnin Johannesburg, inda za su tattauna da jakadun Amurka a tsawon kwana uku.

An zaɓi yin taron na bana ne a Afirka ta Kudu “don nuna alamar jaddada alkawarin dangantakar ɓangarorin biyu,” kamar yadda Joy Basu, mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka a harkokin Afirka ta shaida wa AFP.

TRT Afrika da abokan hulda