Dangote

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya sanar da janye aniyarsa ta shiga kasuwancin ƙarfe a Nijeriya.

Janyewar da hamshaƙin ɗan kasuwar ya yi na zuwa ne watanni biyu bayan kamfaninsa ya sanar da cewa zai zuba jari a ɓangaren sarrafa ƙarafa domin faɗaɗa tattalin arziƙin Nijeriya.

A yayin da yake jawabi ga manema labarai a Legas a ranar Asabar, shahararren mai kuɗin ya bayyana cewa kamfanin nasa ya janye daga wannan kasuwancin ne domin kada a zo ana zargin kamfaninsa da babakere.

Fitaccen ɗan kasuwar ya kuma yi watsi da zargin da ake yi wa wasu kamfanoninsa na babakere a harkokin kasuwanci.

“Kun san kan batun sabon kasuwancin da muka sanar, wanda shi ne na ƙarafa, a gaskiya kamfaninmu ya yanke shawarar cewa ba za mu yi kasuwancin ƙarfe ba domin idan muka yi kasuwancin, za a rinƙa kiranmu da sunaye iri-iri kamar masu babakere,” in ji shi.

“Haka kuma za a bayar da ƙwarin gwiwar shigo da kayayyaki, ba za mu so mu shiga nan ba.”

“Idan kuka dubi duka ayyukanmu a Dangote (Group), muna ƙara ƙima; mukan dauki kayayyaki wanda aka samar da su a cikin ƙasa mu sarrafa su zuwa kayayyakin amfani, mu kuma sayar.

Ba mu taba hana kowa a sane ko cikin rashin sani ba daga yin irin kasuwancin da muke yi. "Lokacin da muka fara kasuwancin siminti, Lafarge ne kawai ke aiki a nan Nijeriya.

Babu wanda ya taba kiran Lafarge a matsayin mai babakere," in ji shi. Shugaban kamfanin na Dangote ya bayyana cewa kiran kamfaninsa da ake yi da mai babakere ba ya yi masa daɗi a ransa.

TRT Afrika