Kasar Chadi ta kasance kasa mai arzikin danyen mai /Photo:Reuters

Gwamnatin Chadi ta yi wa jakadanta a Kamaru kiranye “don tattaunawa” kan zargin da ta yi cewar jami’an Kamaru suna yi mata zagon-kasa kan harkar mai.

Wata sanarwar da sakataren gwamnatin kasar, Dr Gali Ngothe Gatta, ya fitar ranar Juma’a ta nuna damuwar kasar kan yadda kamfanin mai na Kamaru da kamfanin makamashi na Savannah Energy suka tsayar da yarjejeniyar cinikin kashi 10 na kadarar mai da kasar Chadi ba ta yarda da cinikinta ba.

Kwanan baya ne Savanna Energy ya sayi kashi daya cikin hudu na hannun-jarin Exxon Mobil a Kamaru da Chadi.

Gwamnatin Chadi ba ta yarda da cinikin ba wanda ya kai dala miliyan 407 ba, tana mai cewa ya saba wa yarjejeniyar da suka kulla.

Wannan matakin ne ya sa gwamnatin Chadi ta yi shelar karbe iko da duk kadarorin Exxon Mobil a kasar.

Sanarwar ta kara da cewar “Chadi ta samu kanta cikin wani halin da ya wajaba ta kare muradunta tare da yin tir da abubuwan da Kamaru da jami’anta ke yi don kawo nakasu ga huldar da ke tsakanin kasashen biyu.”

Tun da aka fara maganar kamfanin Savannah Energy a Chadi ne alamu suka nuna cewar akwai hannun jami’an Kamaru da jami’an wasu kasashen Afirka da ke son kawo cikas ga Chadi, inji sanarwar.

Ta yi ikirarin cewar Kamaru ba ta amsa duk tambayoyin da Chadi ta yi mata kan abubuwan da ta lura da su kan lamarin ba.

TRT Afrika da abokan hulda