Bankin Raya Kasashen Afirka ya bai wa Kamaru lamunin dala miliyan 80 don ta gina gada

Bankin Raya Kasashen Afirka ya bai wa Kamaru lamunin dala miliyan 80 don ta gina gada

Ana sa ran gadar za ta kasance wata hanyar bunƙasa tattalin arziki tsakanin Kamaru da Equatorial Guinea da kuma Gabon.
AfDB ya bai wa Kamaru tallafin kudi Euro miliyan 73.44 domin gina wata gada a kan Kogin Ntem da ke kan iyaka da Equatorial Guinea. Getty Images 

Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB) ya bai wa Kamaru tallafin kudi Euro miliyan 73.44 domin gina wata gada a kan Kogin Ntem da ke kan iyaka da Equatorial Guinea.

Ginin gadar wani bangare ne na Shirin Gudanar da Kasuwanci da Sufuri na Yanki don hanyar tattalin arziki tsakanin Kamaru, Equatorial Guinea, da Gabon.

AfDB ya ce tallafin kudi ya ƙunshi lamuni daban-daban na Yuro miliyan 48.96 daga Bankin Raya Ƙasashen Afirka da kuma Yuro miliyan 24.48 daga Asusun Raya Ƙasashen Afirka.

Sabuwar gadar, wacce za ta haɗe Campo, a Kamaru, da Rio Campo, a Equatorial Guinea, za ta inganta tsarin jigilar kayayyaki a kan hanyar Yaoundé da Bata da Libreville, a cewar AfDB.

Regional integration

"Taimakon da cibiyar tamu ta bayar yana da nufin faɗaɗawa da kula da hanyoyin sadarwa na zamani a cikin ƙasashen da ke yankin da kuma hanzarta haɗewar yankin," in ji Serge N'Guessan, Darakta Janar na AfDB a Afirka ta Tsakiya, kuma shugaban kasar bankin na ofishin Kamaru.

Shirin na ɗaya daga cikin ayyukan da bankin ya fi bai wa muhimmanci kuma ya yi daidai da ''Dabarun Dogon Zango na 2023-28'' na Afirka, in ji bankin.

Har ila yau, ya yi daidai da ''Dabarun Haɗin Kai na Yankin Tsakiyar Afirka (RISP-CA) 2019-25'', wanda a halin yanzu ana ci gaba da nazarinsa.

Za a fara aikin ne a watan Disambar 2023, tare da kammala aikin a watan Nuwamban 2028.

TRT Afrika