Jami'an tsaro a Kamaru sun kama gungun wasu masu buga jabun kudi a kauyen Moungo da ke yankin birnin Douala.
Rundunar 'yan sandan Souza da ke Moungo ta ce gungun mutanen ya hada da mata hudu, inda aka bayar da sunan uku daga cikinsu kamar haka: Ateme Belogo Genevieve da Djoukoua Nicole da Bedjeu Annabelle, tare da shugaban gungun mai suna Fotieo Etienne Baudelaire.
Rundunar ta ce mutanen sun yi fice wajen "buga jabun kudi da kuma sanya su a kasuwannin Kamaru," in ji rundunar 'yan sandan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Cameroon News Agency ya rawaito ranar Litinin.
"An kama mutanen ne kwanan baya suna buga jabun kudi na FCFA 10,000 da 5,000, da kuma 2,000", inda suke yaudarar mutane wajen karbar kudin.
An kwace kimanin FCFA miliyan 30 daga wurinsu, in ji 'yan sanda.
Kamfanin dillancin labaran ya ce jami'an tsaro sun kama mutanen ne tare da hadin gwiwar 'yan tireda na kasuwar Souza.