Za a yi amfani da kudaden ne wajen tallafa wa kasafin kudin kasar. / Hoto: Reuters

Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ya amince da shirin tallafin dala miliyan 102.6 ga kasafin kudin Ghana, wanda zai mayar da hankali wajen rage basussukanta da kuma farfado da tattalin arzikin kasar, kamar yadda Bankin da Ma'aikatar Kudin Ghana suka bayyana a ranar Alhamis.

Ghana, wacce take da arzikin zinari da koko da kuma fetur, tana tattaunawa da wasu kasashe da masu ba ta lamunin kasuwanci don sake fasalin hanyoyin biyan basussukan da ke kanta a daidai lokacin da take fama da matsalar tattalin arziki mafi muni a baya-bayan nan.

Kasar tana fama da tarin basussuka da suka yi mata katutu.

"Shirin zai taimaka wa ayyukan sauye-sauyen farfado da tattalin arzikin gwamnati ta hanyar inganta fannin kudaden kasar da kuma bunkasa ayyukan yi," a cewar wakiliyar bankin AFDB, Eyeruslen Fasika a wata sanarwa da ta fitar bayan taron rattaba hannu kan yarjeniyar.

Gabatar da kasafin kudi

Shirin ya kara wa Ghana tsarin samun lamuni da take kai a yanzu tare da Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF, a cewar Fasika.

A watan Mayu ne hukumar zartarwa ta IMF ta amince ta ba da rancen dala biliyan 3 ga kasar Afirka ta Kudu cikin shekaru uku, inda bayar da kusan dala miliyan 600 nan take.

Kwararru da dama sun sha bayyana damuwarsu game da sharuddan IMF na lamuni ga kasashe masu tasowa.

Ghana na sa ran za ta sake samun wani kaso bayan yarjejeniyar sake fasalin basussuka da masu bin ta ke yi a hukumance.

Ana sa ran Ministan Kudin Ghana Ken Ofori-Atta zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 a gaban majalisar dokokin kasar a ranar 15 ga watan Nuwamba.

TRT Afrika