Bankin Duniya ya amince da bayar da sabbin bashi har guda uku da suka kai dala biliyan 1.57 ga Nijeriya.
A wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana amince da bayar da bashin ne don ƙarfafa wa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya gwiwa wajen gina ɗan'adam da inganta kula da lafiyar mata, yara da manyan mutane.
Sanarwar ta ƙara da cewa ayyukan da aka amince da su ɗin za su taimaka wajen magance illar sauyin yanayi kamar ambaliyar ruwa da fari ta hanyar ƙarfafa madatsun ruwa da noman rani.
"A yau Bankin Duniya ya amince da bayar da basuka nau'i uku da suka kai dala biliyan 1.57 don taimaka wa Gwamnatin Nijeriya ta ƙarfafa gina ɗan'adam ta hanyar inganta kiwon lafiyar mata, yara ƙanana da ma manya, da kuma magance illar tasirin sauyin yanayi kamar ambaliyar ruwa da fari, ta hanyar ƙarfafa madatsun ruwa da noman rani," in ji sanarwar.
Bankin Duniya ya ce wannan bashin ya haɗa da dala miliyan 500 don magance matsalolin gudanarwa da suke kawo cikas wajen bayar da ilimi da kula da lafiya, dala miliyan 570 na kula da lafiya a matakin farko da wata dala miliyan 500 don samar da makamashi mara gurɓata muhalli da noman rani a Nijeriya.
"Shirye-shiryen 'The Hope Gov da Hope PHC' za su taimaka wa Gwamnatin Nijeriya ta inganta gudanar da ayyuka a ɓangaren ilimi da kula da lafiya a matakin farko, waɗanda suna da matuƙar muhimmanci wajen inganta rayuwar 'yan Nijeriya," a cewar Bankin Duniya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa "Shirin SPIN zai taimaka wa Nijeriya wajen inganta madatsun ruwa da kula da su da samar da makamashi da noman rani a wasu yankunan ƙasar."
"Shirin The HOPE-GOV kuma zai taimaka wa Nijeriya wajen magance matsalolin shugabanci da hanyoyin jagoranci a wasu muhimman ɓangarorin cigaba guda biyu," in ji sanarwar ta Bankin Duniya.
A ranar 26 ga Satumban 2024 aka amince da bayar da bashin da ke da manufar Bankin Duniya na ƙarfafa kyautata rayuwar ɗan'adam a Nijeriya da kuma yaƙi da illolin sauyin yanayi.