Haɓakar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta ƙara ƙaruwa a cikin watan Janairu kuma ta kai kusan kashi 30 cikin 100 a duk shekara, sakamakon tsadar kayan abinci da faduwar darajar da Naira ke yi.
Wasu masana tattalin arziki sun yi imanin cewa bayanan za su iya taimakawa wajen shawo kan Babban Bankin ƙasar ya samar da ƙarin kudin ruwa mai yawa a ƙarshen wannan watan.
Haɓakar farashin kayan masarufi ya tashi a karo na 13 kai tsaye a watan Janairu zuwa kashi 29.90% idan aka kwatanta da bara war haka, daga kashi 28.92 cikin 100 na Disamba, kamar yadda bayanai daga Ofishin Kididdiga na ƙasa suka nuna.
Rabon da a samu hauhawar farashin kayayyaki mai girma irin haka a ƙasar da ta fi kowacce ƙarfin tattalin arziki a Afirka ta kuma fi yawan al’umma a nahiyar, tun shekarar 1996, lamarin da yake ta janyo raguwar kudaden shiga da tanadi, da kuma kara tabarbarewar tsadar rayuwa.
Faɗuwar darajar Naira, wadda ta yi ƙasa sosai a karo na biyu a cikin ƙasa da shekara guda a watan da ya gabata, shi ne babban abin da ke jawo hauhawar farashin, da kuma tsadar makamashi da kayan aiki da ke da alaƙa da matsalolin ababen more rayuwa.
Abinci da kayan sha su ne suka fi komai tsada a watan na Janairu.
Farashin kayan abinci sun tashi da kashi 35.41 cikin 100 a watan Janairu, dafa kashi 33.93 cikin 100 na watan Disamba.
Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirinta na kafa kwamitin ƙayyade farashin kayan abinci don rage raɗaɗin hauhawar farashin da ake fama da ita.