Sama da kamfanunnuka 40 ne suka baje hajarsu a wajen kasuwar baje-kolin. Photo: TRT Afirka

Ana ci gaba da gudanar da babban taron kasuwanci a birnin Istanbul na Turkiyya da manufar habaka dangantakar cinikayya tsakanin kasar da nahiyar Afirka.

Taron Kasuwanci da Afirka tare da tallata kayayyaki ya tattara kamfanoni sama da 40 na Turkiyya da ke nuna hajojinsu a bangarorin tufafi da matsattsun kayan marmari da fasahar kere-kere da makamashi da ilimi, da ma bayar da shawarwari kan sha'anin kudade.

Taron da Kungiyar 'Yan Kasuwar Afirka-Turkiyya ta shirya, kuma kamfanin Beam na Turkiyya da Bankin NCBA na Gana suka dauki nauyi, ya samu mahalarta da dama da ke nuna muhimmanci karfafa alakar Turkiyya da Afirka.

"Turkiyya kasa ce mai muhimmanci. Idan ka duba Turai, Asia d Afirka, za ka samu yankin da ya hade su waje guda, shi ne Istanbul," in ji shugaban TABA Mr. Fatih Akbulut yayin bayanin bude taron baje-kolin.

Jarin kasuwanci tsakanin Turkiyya da Afirka ya karu zuwa kusan dala biliyan 30 a yanzu haka, daga dala biliyan 4.5 a 2005, kuma kasuwanci na bunkasa a tsakanin bangarorin biyu, in ji Akbulut.

Turkiyya na fatan wannan jari na kasuwanci zai kai dala biliyan 50 a shekaru masu zuwa.

Sakamakon nasara

Ya ce Turkiyya ta zama kawar Afirka mai matukar amfani d amuhimmanci - madalla ga manufofin shugaba Recep Tayyip Erdogan na zurfafa alakar Afirka da Turkiyya a shekaru 20 da suka gabata.

Akbulut ya kara da cewa "A yanzu haka kamfanin jiragen saman Turkiyya na zuwa garuruwa 64 a kasashen Afirka. Wannan ci gaba ne mai muhimmanci sosai."

Wannan na bayar da gudunmowa sosai wajen kai komon kayayyaki da ayyuka tsakanin kasashen Afirka da Turkiyya. Tare da ofisoshin jakadancinta 44 a Afirka, Turkiyya ta habaka alakarta a nahiyar.

"Alakar Turkiyya da Afirka ta yi karfi sosai a shekaru 20 da suka gabata. Tsare-tsarenmu game da Afirka da hadin kan da aka yi bayan hakan sun kawo nasara da sakamakon mai kyau wajen zurfafa alaka da hadin kan mu da nahiyar," in ji Farfesa Cuneyt Yuksel, shugaban kwamitin shari'a na majalisar dokokin Turkiyya a yayin gabatar da jawabi ga mahalarta baje-kolin.

Damarmaki

Yuksel ya kara da cewa "Turkiyya ta kasance tare da al'ummar Afirka a yayin bukatarsu ta fadada ci gaba da habakarsu, wanda hakan ne ya sanya muke da wakilcin diflomasiyya a dukkan nahiyar."

Ya kuma yi tsokacin cewa Turkiyya na ci gaba da bayar da gudunmowa wajen cigaban tattalin arziki da zamantakewa da samar da kayan more rayuwa a Afirka, ta hanyar amfani da hukumominta na gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da bangaren 'yan kasuwa masu zaman kansu.

Ya jaddada cewa "Mu ma muna da abubuwa da dama da za mu kwaikwaya daga Afirka."

Ministan Kasuwanci da Masana'antu na Guinea Bissau Joao S. Handem Junior ya bukaci masu zuba jari na Turkiyya da su bibiyi damarmakin da ake da su a Afirka, musamman a kasarsa ta hanyar hadin kan da zai amfani juna, inda ya bayyana noma a matsayin bangare mai muhimmanci a kasarsa.

Ministan ya ce "Muna son koyon yadda za mu inganta sashen nomanmu daga wajen Turkiyya. Guninea Bissau na da kasa mai albarka, kuma noma ne hanyar da ta fi kawo mata kudaden shiga,"

Kawo sauyi

Minista Junior ya kuma ce kasarsa za ta ci gaba da hada kai da Turkiyya a dukkan bangarori, inda ya kuma yi tsokaci kan alakar amfanar juna ta Turkiyya da Afirka.

Mahalarta da dama daga Afirka na halartar baje-kolin a birnin Istanbul na hada-hadar kasuwanci da ke Turkiyya.

Dr. Adamu Abdullahi, dan kasuwa daga Kamaru ya bayyana farin cikinsa kan yadda nahiyar Afirka ke kara zama wajen da 'yan kasuwar Turkiyya suka karkata.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Akwai bukatar mu kara zage damtse wajen amfana da dukkan damarmakin kasuwanci da ke tsakanin Afirka da Turkiyya.

Afirka na da abubuwa da dama da Turkiyya ke bukata, haka ma Afirka za ta koyi abubuwa da yawa daga Turkiyya don ci gabanta."

A nasa bangaren, Jakadan Libiya a Ankara Hassan El-Gelaib ya ce tare da albarkatun kasa masu yawa da dumbin jama'a, Afirka za ta iya zama mai kawo sauyi a nan da wani lokaci mai zuwa.

TRT Afrika